Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus

Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus

Wani mutumi mai shekaru 55 a duniya ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas LASUTH, Idi Araba, sakamakon cutar Coronavirus. Punch ta ruwaito.

A cewar Punch, Majiya a asibitin ya bayyana cewa sai bayan mutuwarsa aka gudanar da gwaji aka gano cewa yana dauke da cutar Coronavirus a jikinsa.

Yace: "An gudanar da gwajin garkuwar jiki ta alamar yatsu kuma na tabbatar da cewa yana da cutar COVID-19."

Ya kara da cewa mutumin wanda ya kasance yana fama da cutar koda ya kwanta a asibitin ne ranar Alhamis.

Amma masu jinyarsa suka ki bayyanawa asibitin ainihin abinda ke damunsa da kuma irin tafiye-tafiyen da yayi zuwa kasar waje a makonni baya-bayan nan sai bayan mutuwarsa.

KU KARANTA: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

Majiya ya cigaba da cewa: "Mutumin bai bayyana tafiye-tafiyen da yayi ba ko kuma kila ya hadu da wani wanda yayi tafiya kasar waje ba."

"Ya fadawa likitoci cewa ba ya fama tari, wahalar numfashi, ciwon gabobin jiki ko gudawa."

"Amma bayan mai rijistan asibitin ya bayyana masa abubuwan da suka gano a jikinsa, mutumin ya bayyana gaskiyar cewa lallai da yiwuwan ya kamu da cutar COVID-19 saboda tafiyar da yayi kasar waje."

"Ya bayyana cewa tun lokacin da ya dawo daga kasar Holan makonni biyu da suka shude yake fama da tari."

"Da aka kalubalanci yan uwansa bayan ya mutu, sun bayyana cewa lallai sun boye gaskiyar abinda yake fama da shi ne saboda suna tsoron asibitin ba zata karbeshi idan suka fadi gaskiya."

Mutumin ya mutu da safen nan kuma an tafi da gawarsa.

Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus

Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus

Mutum daya ya kara mutuwa sakamakon Coronavirus
Source: Facebook

A bangare guda, an samu karin mutane ashirin (20) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Juma'a.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita ranar Juma'a inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin (20) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 11 a Legas, 3 a Abuja, 3 a Edo, 2 a Osun, 1 a Ondo.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel