Coronavirus: Mun gano kimanin mutane 3550 cikin 5000 da muke nema - Gwamnatin tarayya

Coronavirus: Mun gano kimanin mutane 3550 cikin 5000 da muke nema - Gwamnatin tarayya

A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta samu nasarar gano mutane 3,550 cikin 5000 da ake nema wadanda suka hadu da tabbatattun masu dauke da cutar Coronavirus.

Dirakta Janar na cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya, Dakta Chikwe Ihekwaezu, ya bayyana hakan a hira da manema labarai da kwamitin kar ta kwanan yaki da COVID-19 ta shirya a birnin tarayya Abuja.

Za ku tuna cewa a ranar Talata, Iheakwaezu ya bayyana cewa ana neman mutane 5000 doin akwai yiwuwan sun kwashi cutar daga jikin wasu tabbatattun masu cutar.

Ya ce wajibi ne a nemo mutanen saboda takaita yaduwar cutar cikin unguwanni.

Yace: "Mun gano kashi 71% na mutanen da muke nema. Amfanin wannan makonni biyu na zaman gida kenan."

"Mutanen farko da suka kamu da cutar sun hadu da mutane da yawa. Yawancinsu cikin jirgi suka hadu kuma wajibi ne mu nemo dukkan wadanda suka shiga jiragen kuma dukkan wadanda muka gano sun hadu da wasu mutane kimanin 30 zuwa 40 daban."

Coronavirus: Mun gano kimanin mutane 3550 cikin 5000 da muke nema - Gwamnatin tarayya

Coronavirus: Mun gano kimanin mutane 3550 cikin 5000 da muke nema - Gwamnatin tarayya
Source: UGC

A bangare guda, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan dokar hana walwala da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka a ranar 29 ga watan Maris. Ya ce za a kara kwanaki matukar 'yan Najeriya ba su kama kansu ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da kwamitin shugaban kasan na yaki da cutar coronavirus yayi a Abuja a ranar Juma'a, 3 ga watan Afirilu.

Lai Mohammed ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji hada taruka kuma a dinga tsaftace jiki. Ta hakan ne kadai kowa zai koma al'amuran shi hankali kwance nan da kwanaki 14.

Lai Mohammed ya ce: "Idan bamu kama kanmu ba, akwai yuwuwar a kara kwanakin dokar hana walwalar. Amma idan mun kama kanmu, ba dole bane a kara amma muna fatan hakan."

"Idan muka zauna gida na makonni biyu kuma muna hana yaduwar cutar, komai zai wuce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel