Ba zamu baiwa iyalan duk wanda ya mutu sakamakon Coronavirus gawar ba - Lai

Ba zamu baiwa iyalan duk wanda ya mutu sakamakon Coronavirus gawar ba - Lai

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba zata bayar da gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar Coronavirus ga iyalansu domin birnesu ba.

Ya ce ma'aikatar kiwon lafiya za ta birne saboda ana iya kamuwa da cutar daga cikin mamaci.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a taron kamfanin dillancin labarai NAN a Abuja.

A cewar NAN, ministan ya yabawa yan Najeriya bisa biyayyar da suka yiwa gwamnati kan dokar hana fita.

Yace: "Coronavirus cuta ce mai matukar hadari; har yanzu ba'a samu maganinta ba kuma ta nada ikon kisa, gajiyar da sashen kiwon lafiya da kuma karya tattalin arziki."

"A wasu kasashe cikin firji ake ajiye gawawwaki saboda dakunan ajiye gawawwaki sun cika. Yan Najeriya su sani cewa wannan ba irin gawawwakin da za'a basu bane su birne saboda hakkin ma'aikatar kiwon lafiya ne."

Ba zamu baiwa iyalan duk wanda ya mutu sakamakon Coronavirus gawar ba - Lai
Lai Mohammed
Asali: Facebook

KU KARANTA: Masu cutar Coronavirus 6 sun gudu da inda aka killacesu a Osun

A bangare guda, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya ja kunnen 'yan Najeriya a kan dokar hana walwala da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka a ranar 29 ga watan Maris. Ya ce za a kara kwanaki matukar 'yan Najeriya ba su kama kansu ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da kwamitin shugaban kasan na yaki da cutar coronavirus yayi a Abuja a ranar Juma'a, 3 ga watan Afirilu.

Lai Mohammed ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji hada taruka kuma a dinga tsaftace jiki. Ta hakan ne kadai kowa zai koma al'amuran shi hankali kwance nan da kwanaki 14.

Lai Mohammed ya ce: "Idan bamu kama kanmu ba, akwai yuwuwar a kara kwanakin dokar hana walwalar. Amma idan mun kama kanmu, ba dole bane a kara amma muna fatan hakan."

"Idan muka zauna gida na makonni biyu kuma muna hana yaduwar cutar, komai zai wuce."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel