Annobar Corona: Dan majalisar Bauchi ya sadaukar da albashinsa N476,000 domin yaki da cutar

Annobar Corona: Dan majalisar Bauchi ya sadaukar da albashinsa N476,000 domin yaki da cutar

Wani dan majalisar dokokin jahar Bauchi dake wakiltar al’ummar mazabar Bagoro, Musa Nakwada ya bayyana albashinsa a matsayin dan majalisa, sa’annan ya sadaukar da makudan kudin domin ganin an yaki annobar Coronavirus a jahar.

Daily Trust ta ruwaito dan majalisa Musa Nakwada ya bayyana cewa ya bayar da kafatanin albashin na N476,000 ga kwamitin ko-ta-kwana da gwamnatin jahar Bauchi ta samar domin yaki da cutar Coronavirus, watau COVID-19.

KU KARANTA: Hukumar NCDC ta bayyana babban kalubalen da take fuskanta daga masu cutar Corona

Annobar Corona: Dan majalisar Bauchi ya sadaukar da albashinsa N476,000 domin yaki da cutar
Musa Nakwada
Asali: Facebook

A cewarsa, ya yi haka ne domin taimaka ma wannan kwamiti domin gudanar da aikinta na kare yaduwar cutar a jahar, wanda ta tilasta ma gwamnan jahar, Sanata Bala Muhammad killace kansa bayan ya kamu da cutar.

Haka zalika kungiyar lauyoyin jahar Bauchi da kuma kungiyar matasan yan kwaikwayo na jahar Bauchi sun bayar da kyautar N500,000 ga gwamnatin jahar Bauchi domin cigaba da kokarinta na yaki da cutar Coronavirus.

Jagoran kungiyar lauyoyin jahar Bauchin, Jibrin S Jibrin ya bayyana cewa sun bayar da gudunmuwar ne domin taimaka ma gwamnatin jahar wajen yaki da cutar wanda a yanzu haka ya shafi tattalin arzikin jahar.

Da yake nasa jawabi yayi karbar kudaden, shugaban kwamitin ko-ta-kwana a kan Coronavirus da zazzabin Lassa, kuma mataimakin gwamnan jahar Bauchi, Sanata Baba Tela ya bayyana godiyarsa ga kungiyoyin bisa kokarin da suka yi, sa’annan ya yi alkawarin kashe kudin yadda ya kamata.

Daga karshe ya tabbatar musu da cewa gudunmuwar zai taimaka ma kwamitin wajen shawo kan matsalar da suke ciki sakamakon yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo ta sanar da kama wani shugaban jam’iyyar APC a matakin mazaba a jahar Edo, Mista Sunday Erhabor da yunkurin damfarar jama’a da sunan basu tallafin gwamnati.

Daily Trust ta ruwaito Yansandan sun kama Sunday ne yayin da yake karbar bayanan asusun bankunan jama’a tare da sunayensu da sunan wai sama musu tallafin da gwamnati ta tanada domin rage ma jama’a radadin mawuyacin halin da aka shiga sakamakon bullar annobar Coronavirus.

Da wannan shiri na gwamnati ne Sunday ya fake yana bin jama’a yana amsan bayanan bankunansu, inda yake ikirarin cewa gwamnatin jahar ce ta sanya shi gudanar da wannan aiki, kuma a madadin shuwagabannin jam’iyyar na matakin karamar hukumar yake wannan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel