Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 6 sun kamu da cutar Coronavirus, jimilla 190
Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane shida da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a yau Juma'a, 3 ga Afrilu, 2020.
Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Juma'a inda tace: “An tabbatar da mutane shida sun kamu da #COVID19 a jihar Osun, Najerya.“
“Dai-dai Karfe 11:00 na daren 3 ga Afrilu, mutane 190 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami ashirin, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“
Ga jerin jiha-jiha:
Lagos- 98
Abuja - 38
Osun- 20
Oyo- 8
Akwa Ibom- 5
Ogun- 4
Edo- 4
Kaduna- 4
Bauchi- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-1
Benue- 1

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng