Yanzu-yanzu: An sallami mutane 11 daga asibiti a Legas bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 11 daga asibiti a Legas bayan sun warke daga Coronavirus

- Tabarkallah! Mutane tara sun sake warkewa da muguwar cutar Coronavirus da ta addabi duniya

- Gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa sun sallami marasa lafiyan a ranar Alhamis

- An yi jinyarsu ne a asbitin jinyar cututtuka dake Yaba

Gwamnatin jihar Legas ta alanta sallamar masu fama da cutar Coronavirus 11 daga asibitinta dake unguwar Yaba.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis, 2 ga Afrilu, 2020.

A cewar Sanwo-Olu, marasa lafiya maza tara ne da mata biyu.

Yace: "Ina farin cikin bayyana muku, al'ummar jihar Legas cewa mun sallami marasa lafiya 11 daga asibitinmu dake Yaba."

"Sun samu isasshen lafiya, sun warke kuma gwaji ya nuna cewa sun tsira daga cutar COVID19 kuma tuni tun tafi gidajensu."

"Marasa lafiyan sun hada da maza tara da mata biyu. Sakamakon gwaji biyu da aka gudanar ya nuna cewa basu dauke da cutar."

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 11 daga asibiti a Legas bayan sun warke daga Coronavirus
Coronavirus
Asali: UGC

Shugaban kungiyar likitoci a Najeriya, Aliyu Sokomba, ya ce daya daga cikin mambobin kungiyarsa mai jinyar masu cutar Coronavirus ya kamu da cutar daga jikin mara lafiya.

Sokomba a hirar da yayi da tashar Channels TV ranar Alhamis ya ce likitan ma'aikaci ne a asibitin koyarwan Irrua dake jihar Edo.

Ya ce wajibi ne a rika lura da ma'aikatan kiwon lafiya dake jinyar masu cutar Coronavirus da zazzabin Lassa muddin kasar na son cigaba.

Yace: "A yanzu, ma'aikatan kiwon lafiya na iyakan kokarinsu ta hanyar takaita yaduwar cutar amma su rayukansu na cikin hadari,"

"Daya daga cikin ma'aikatanmu ya mutu jiya sakamakon zazzabin Lassa. Haka rayuwan ma'aikatan kiwon lafiya ya koma a kasar nan."

"A jiya kuma, daya daga cikin Likitocinmu dake ISTH Iruaa, ya kamu da cutar COVID-19. Hakan na nufin cewa kawai ana barin likitocin na kamuwa da cutar kuma babu wanda ya damu da su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel