Coronavirus: Najeriya ta yi nadamar rokon na'uarar 'ventilator' daga attajirin Amurka

Coronavirus: Najeriya ta yi nadamar rokon na'uarar 'ventilator' daga attajirin Amurka

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye rokon da Ma'aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren kasa ta yi na neman tallafin na'uarar taimakawa numfashi ta 'ventilator' daga wurin attajirin kasar Amurka, Elon Musk domin yi wa masu fama da cutar coronavirus magani a Najeriya.

Mai kamfanin SpaceX kuma babban injiniyan kamfanin, Musk, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamisa cewa kamfaninsa tana da raran na'urorin taimakawa numfashin da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na Amurka (FDA) suka amince da ingancinsu.

"Muna da rarar ventilators da FDA ta amince da ingancin su. Za mu aike da asibitoci a kasashen duniya da kamfanin Tesla ke harka da su. Abinda muke bukata kawai shine a yi amfani da su nan take a taimakawa masu jinya ba wai a ajiye su a dakin ajiya ba," kamar yadda ya rubuta a Twitter.

DUBA WANNAN: An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

Jim kadan da wallafa rubutun sa, ma'aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasar ta nuna tana sha'awar samun tallafin daga gare shi inda ta ce tana bukatar a kalla na'urorin kimanin 100 zuwa 500.

Ma'aikatar ta rubuta cewa, "Gwamnatin Tarayyar Najeriya tana bukatar tallafin na'urorin ventilators 100 zuwa 500 domin taimakawa wadanda ke kamuwa da covid-19 a kowanne ranara a Najeriya."

Sai dai bayan wasu 'yan Najeriya sun nuna bacin ransu game da lamarin, mai bawa ministan sharwara na musamman kan kafafen watsa labarai, Yunusa Tanko Abdullahi ya fitar da sanarwar cewa an yi nadamar sakon da aka wallafa da shafin Twitter na ma'aikatar kana an janye batun.

Ya rubuta cewa, "An wallafa wani sako ta shafin Twitter na Ma'aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren kasa ba tare da izini ba.

"An yi nadamar wallafa sakon hakan ya sa aka janye shi. Za mu tabbatar cewa mun yi bita kan yadda muke gudanar da harkokin mu na cikin gida domin tabbatar da cewa hakan ba zai sake faruwa a nan gaba ba.

"Mun yi nadamar afkuwar kuskuren."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel