Da duminsa: Direban da ya kamu da Coronavirus a Minna ya gudu daga inda aka killaceshi

Da duminsa: Direban da ya kamu da Coronavirus a Minna ya gudu daga inda aka killaceshi

Wani direban motan haya da ya kamu da cutar Coronavirus ya gudu daga inda aka killaceshi a garin Bida, jihar Neja kuma na bazama nemansa yanzu.

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Mohammed Makunsidi, ya alanta nemansa ruwa a jallo kuma gwamnati ta nada kwamiti na musamman domin nemoshi.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a Minna, Makunsidi yace: "Mun yi mamakin guduwarsa kuma yadda ya gudu daga asibitin abin mamaki ne garemu har yanzu amma an harzuka wajen kamoshi."

"Mun samu labarin cewa ya gudu cikin Bida, kuma muna biye da shi yanzu. Mambobin hukumar yaki da COVID-19 da jami'an ma'aikatar lafiya na Bida yanzu domin nemansa da kuma tabbatar da cewa ya yi abinda cibiyar NCDC ta umurcesa."

Kwamishanan ya kara da cewa an killace wasu mutane biyu da suka dawo daga kasar Birtaniya da Canada a garin Kontagora kuma ana gwada su."

Da duminsa: Direban da ya kamu da Coronavirus a Minna ya gudu daga inda aka killaceshi
Direban da ya kamu da Coronavirus a Minna ya gudu daga inda aka killaceshi
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta bawa 'yan Najeriya miliyan 11 tallafi

A bangare guda, Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, ya umurci jami’an tsaro da su bindige duk wanda ya dawo jahar sannan ya yi kokarin guduwa daga inda ake killace mutane.

Gwamnatin jahar a karshen makon da ya gabata ta yi umurnin gaggawan killace akalla mutane 37 da suka shigo jahar ta daji bayan gwamnatin jahar ta yi umurnin rufe iyakokinta.

Gwamnatin jahar ta yi umurnin cewa a gaggauta rufe dukkanin iyakoki a jahar domin hana yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Gwamnan ya kara da cewar a bindige duk wani bako da ya dawo sannan ya yi kokarin guduwa daga cibiyar killace mutane wanda a nan ne za a dunga yi musu gwaji a kullun har tsawon kwanaki 14 biyo bayan barkewar annobar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel