Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe kanta akan mijinta yayi mata kishiya

Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe kanta akan mijinta yayi mata kishiya

- Ruka kyakyawar mata ce mai shekaru 30 a duniya kafin mutuwarta kuma mahaifiyar yara biyu

- Ta halaka kanta ne kuwa inda ta bar yara biyu sakamakon bakin mummunan kishinta

- Duk da Ruka ta tarar da uwargida, amma ta ga ba za ta iya jure wa mijinta ya zauna da sabuwar amaryar da yayi ba

Ruka kyakyawar mata ce mai shekaru 30 da ta bar yaranta biyu a duniya. Bakin ciki tare da mugun kishi ne suka sa mahaifiyar yaran biyu ta halaka kanta.

Kamar yadda wata wallafa a shafin Tinuola Tolani a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ta bayyana, Ruka ce mata ta biyu a wajen mijinta kuma tana da yara biyu.

Ruka ba ta iya jure kishi ba don bayan mijinta ya tare da matarshi ta uku, sai ta halaka kanta.

Ba wannan bane karo na farko da mata suke kashe kansu ba saboda tsananin kishi.

KU KARANTA: Yadda wani likitan kasar Amurka ya warkar da masu cutar Coronavirus 500 da maganin zazzabin cizon sauro

A kwanakin baya Legit.ng ta ruwaito yadda wata mata da ke Unguwar Rimin Gado a jihar Kano ta babbaka kanta saboda tsananin kishi.

Matar mai suna Rabi ta kashe kanta ne bayan da mijinta ya tare da sabuwar zukekiyar amaryar shi.

Kamar yadda labarin ya bayyana, Rabi ta fitar da yaranta daga dakinta ne da sassafe, inda ta samu fetur ta bankawa kanta tare da kyasta ashana.

Wannan lamarin kuwa ya jawo babbakewarta inda ta halaka har lahira.

Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe kanta akan mijinta yayi mata kishiya

Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe kanta akan mijinta yayi mata kishiya
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel