Yanzu-yanzu: An sallami mutum na farko daya kamu da COVID-19 a Ekiti

Yanzu-yanzu: An sallami mutum na farko daya kamu da COVID-19 a Ekiti

Gwamnatin jihar Ekiti ta sanar da cewa an sallami mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus da mai kula da shi daga cibiyar killace masu cutar a jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita ranar Talata inda tace mutumin ya tafi gida bayan kwashe kwanaki 12 a killace.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Mojisola Yaya-Kolade, da wata jami'ar UNICEF suka rakasu bayan an sallamesu.

Yanzu-yanzu: An sallami mutum na farko daya kamu da COVID-19 a Ekiti (Hotuna)
An sallami mutum na farko daya kamu
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: An sallami mutum na farko daya kamu da COVID-19 a Ekiti (Hotuna)
An sallami mutum na farko daya kamu da COVID-19
Asali: Facebook

A bangare guda, Gwamnatin jihar Oyo ta alanta cewa mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar ya samu sauki kuma an sallamesa.

Wannan ya biyo bayan labarin tabbatar da kamuwar gwamnan jihar, Seyi Makinde, da cutar.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar, Taiwo Adisa, ya bayyana cewa “An sallami wanda ya fara kamuwa da cutar COVID-19 da aka killace.”

“An sallameshi ne bayan kammala jinyarsa a cibiyar killace mutane dake asibitin Agbami Chest dake Ibadan, babbar birnin jihar.”

“Gwajin Mara lafiyan wanda ya dawo daga kasar Amurka na biyu ya nuna cewa ya warke daga cutar.”

Jawabin shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar Oyo, Taiwo Ladipo, ya bayyana cewa mutumin ya kwashe kwanaki shida a killace yana jinya har ya samu lafiya.

Yace: “Ya samu lafiya kuma ya koma gidansa. Ma’aikatan kiwon lafiya zasu rika zuwa gidansa dubashi”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel