Labari da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan dokar Covid-19

Labari da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan dokar Covid-19

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a daren jiya Alhamis ya saka hannu kan wata doka ta ayyana Covid-19 a matsayin annoba mai hatsari a duniya.

Sanarwar ta mai bawa shugaban kasar shawara na musamman kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ta ce shugaban kasar ya yi amfani da ikon da kudin tsari mulki ta bashi a sashi na 2,3 da 4 na Quarantine Act (CAP Q2 LFN 2004) ya rattaba hannu a kan dokar Covid-19 a ranar Litinin

Dokar da za ta fara aiki daga ranar 30 ga watan Maris na 2020 za ta bawa gwamnati izinin aiwatar da mafi yawancin matakan da shugaban kasa ya lissafa a jawabin da ya yi wa 'yan kasa a ranar 29 ga watan Maris na 2020 da suka hada da Takaita ko hana zirga-zirga a Legas, Abuja da Ogun a matsayin mataki na takaita yaduwar annobar a kasar.

Labari da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan dokar Covid-19
Labari da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan dokar Covid-19
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: COVID-19: Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar cewa za a raba wa 'yan Najeriya N30,000

Kazalika, dokar ta bawa bankuna da wasu hukumomi masu hada-hada da kudade damar yin harkokinsu ta intanet wato yanar gizo da saka kudade a na'uarorin ATM da abokan huldarsu za su rika amfani da shi duk da dokokin da aka saka a kasar na takaita ayyuka da hada-hada a kasar.

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi alkawarin bayar da kyautan zunzurutun kudi har Naira miliyan 2 a matsayin tukwici ga duk wanda ya bayar da bayannai da su taimaka a ceto dan uwansa da aka sace.

The Nation ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi awon gaba da yayan gwamnan, Adamu Mohammed.

An ruwaito cewa an sace shi na misalin karfe 7 na yamma a Kobo Streer da ke birnin Bauchi a ranar Laraba 25 ga watan Maris na shekarar 2020.

Mai bawa gwamna shawara na musamman a kan sabuwar kafar yada labarai, Mukhtar Gidado ne ya bayar da wannan sanarwar tukwicin da za a bawa duk wanda ya bayar da bayyanan da suka taimaka aka ceto yayan gwaman cikin koshin lafiya cikin sakon da ya raba wa manema labarai a Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel