Yanzu-yanzu: Mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a Oyo ya samu sauki, an sallamesa

Yanzu-yanzu: Mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a Oyo ya samu sauki, an sallamesa

Gwamnatin jihar Oyo ta alanta cewa mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar ya samu sauki kuma an sallamesa.

Wannan ya biyo bayan labarin tabbatar da kamuwar gwamnan jihar, Seyi Makinde, da cutar.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar, Taiwo Adisa, ya bayyana cewa “An sallami wanda ya fara kamuwa da cutar COVID-19 da aka killace.”

“An sallameshi ne bayan kammala jinyarsa a cibiyar killace mutane dake asibitin Agbami Chest dake Ibadan, babbar birnin jihar.”

“Gwajin Mara lafiyan wanda ya dawo daga kasar Amurka na biyu ya nuna cewa ya warke daga cutar.”

Jawabin shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar Oyo, Taiwo Ladipo, ya bayyana cewa mutumin ya kwashe kwanaki shida a killace yana jinya har ya samu lafiya.

Yace: “Ya samu lafiya kuma ya koma gidansa. Ma’aikatan kiwon lafiya zasu rika zuwa gidansa dubashi”

Yanzu-yanzu: Mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a Oyo ya samu sauki, an sallamesa

An sallamesa
Source: UGC

KU KARANTA: Rundunar Sojin Najeriya sun hallaka babban kwamandan Boko Haram, Abu Usamah

A jiya, Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane ashirin da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Litinin inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin sun kamu da #COVID19 a Najerya. 13 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Kaduna, .“

“Dai-dai Karfe 9:o0 na daren 30 ga Maris, mutane 131 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami takwas, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“

Ga jerin jiha-jiha

Lagos- 81

FCT- 25

Ogun- 3

Enugu- 2

Ekiti- 1

Oyo- 8

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-2

Rivers-1

Benue- 1

Kaduna- 3

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel