Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun kone ofishin Yan sanda a Katsina (Hotuna)
Daruruwan matasa ne suka ci karo da 'yan sanda a karamar hukumar Kusada da ke jihar Katsina a kan damke wani limamin garin da aka yi.
'Yan sandan sun kama limamin sakamakon karantsaye da yayi ga dokar gwamnatin jihar da ta hana kowanne taron addinin a matsayin hanyar hana yaduwar muguwar cutar coronavirus.
Majiya mai karfi ta bayyana cewa wasu 'yan sandan sun ziyarci gidan malamin ne mai suna Malam Hassan. Sun bukaci tafiya da shi don amsa tambayoyi a kan dalilin da yasa ya yi jam'in, lamarin da mazauna yankin basu so ba.

Asali: Twitter
Abinda 'yan sandan suka yi kuwa ya matukar fusata matasan, wanda yasa har suka bi su ofishinsu a Kusada. Bayan yunkurin kwace Malam daga hannun 'yan sandan ya gagara, sai suka bankawa ofishin 'yan sandan wuta har hakan ya jawo mutuwar dan sanda daya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Coronavirus: Kotu ta aike da matar da ta yi wa dan sanda tari a fuska zuwa gidan yari

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, SP Gambo Isah ya ce kungiyar matasan ta shirya kanta ne ta yadda za su yi zanga-zanga tare da harar 'yan sandan. Sun kuwa yi nasara inda suka fi karfin 'yan sandan da ke aiki har suka kone ofishin.
Sun kara da kone motoci bakwai da babura goma wadanda ke karkashin kular 'yan sandan.
Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan ya sanar, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Sanusi Buba ya bada umarnin tura rundunar sintiri da kuma rundunar hadin guiwar ta 'yan sandan don tabbatar da zaman lafiya ya dawo a jihar.
"An damke matasa 90 masu zanga-zanga yayin da mutum daya ya rasa ransa. A halin yanzu ana ci gaba da bincike," ya kara da cewa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng