Jaruman Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 100, sun yi rashin Soji 29

Jaruman Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 100, sun yi rashin Soji 29

Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa hare-haren jirgin sama na rundunar Operation Lafiya Dole, ta kai ya yi sanadin halakan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram 1000 a batakashin da akayi ranar Litinin, a garin Gorgi, jihar Borno.

Jawabin ya ce hukumar ta yi rashin Sojoji 29 yayinda 39 suka jikkata a artabun.

Karin bayani kan lamarin, diraktan yada labarin ma’aikatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana cewa sabanin jawabin da yayi da farko cewa 47 aka kashe, rahoto daga filin daga ya nuna cewa basu kai haka ba, 29 kadai aka kashe.

Yace: “Bayan harin, an samu wadannan rahotannin: An kashe Sojojin Najeriya 29 a faggen fama, an jikkata 39 a faggen daga sakamakon tashim bam cikin motar da ke dauke da makaman da aka kaiwa Sojojin.”

“Hakan ya sabawa adadin da muka fada da farko cewa mutane 47 aka kashe kuma 15 sun jikkata. Hakan na faruwa a lokacin yaki saboda gudun kada masu yada labaran karya su fadi adadin da bashi bane.”

KU KARANTA Gwamnatin jihar Plateau ta gargadi Yahaya Jingir

Jaruman Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 100, sun yi rashin Soji 29
Maj Gen Eneche
Asali: Original

A bangare guda, Wasu 'yan bindiga ne sun sace Ango da abokanansa guda biyar akan hanyar Wukari-Ibi dake jihar Taraba a jiya Juma'a da yamma, mutanen yankin sun sanarwa da Premium Times

Mutanen da lamarin ya shafa dai suna kan hanyarsu ta dawowa daga wajen daurin auren ne a Gboko, cikin jihar Benue, kwatsam sai gani suka yi an dakatar da motarsu a kauyen Dan-Wanzam.

Wani babba a yankin da ya nemi a boye sunanshi shine ya bayyana hakan.

A yanzu haka dai matasa da sauran mutane na yankin sun hada kai zasu fuskanci 'yan bindigar domin ayi ta ta kare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel