Annobar Corona: Gwamnan jahar Oyo ya sanya dokar ta baci a jahar gaba daya

Annobar Corona: Gwamnan jahar Oyo ya sanya dokar ta baci a jahar gaba daya

Gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya sanya dokar ta baci tare da hana jama’a fita daga gidajensu har sai yadda hali yayi sakamakon bullar annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam, a jahar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito gwamnan ya sanar da wannan doka ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris bayan hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC ta sanar da samun mutane uku dake dauke da cutar a jahar Oyo.

KU KARANTA: Gwamnan Nasarawa, mataimakinsa da Sarkin Lafiya sun tsira daga Coronavirus

Gwamnan yace: “Da wannan dalili, na sanya dokar hana shiga da fita daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe, ban yarda a yi taron da ya haura na mutane 10 a duk fadin jahar Oyo ba. Daga ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, za mu kulle kasuwanni, illa masu sayar da abinci.

“Haka zalika na dakatar da tafiye tafiye daga ciki da wajen jahar, sai dai motocin dake dauke da kayan abinci, magani da man fetir, dokokin nan zasu fara aiki ne daga tsakar daren Lahadi, kuma zamu dinga duba su lokaci zuwa lokaci.” Inji shi.

A cewar gwamnan, an samu mutane 84 da ake zargin suna dauke da kwayar cutar, kuma tuni an fara bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da su, tare da gudanar da gwaje gwaje a kansu.

A wani labarin kuma, Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta kara tabbatar da sabbin mutane 11 da suka kamu ta kwayar cutar Covid-19 wato coronavirus a kasar.

An samu karuwar mutane takwas ne a Legas sannan guda biyu a Enugu sai kuma daya a jihar Edo. Hakkan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar a halin yanzu ya kai 81.

A cewar hukumar ta NCDC, "An samu sabbin mutane 11 da suka kamu da Covid-19 a Najeriya; 8 a jihar Legas, 2 a Enugu da kuma guda daya a jihar Edo kawo yanzu a ranar 27 ga watan Maris na 2020 misalin karfe 11.55 na dare, jimlar wanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar 81. An sallami mutane 3 sai kuma mutum daya ya mutu."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel