Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus na Adams Oshiomhole ya fito

Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus na Adams Oshiomhole ya fito

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Comrade Adams Oshiomhole ba ya dauke da kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna.

Sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar Lanre Issa Onilu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja.

Onilu ya ce sakamakon kokwanto da ake yi kan yiwuwar cudanya da shugaban jam'iyyar na APC na kasa ya yi da wasu da aka gano suna dauke da cutar, Oshiomhole ya tafi an masa gwajin kwayar cutar a ranar Alhamis kuma yanzu sakamakon ya fito baya dauke da ita.

Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus na Adams Oshiomhole ya fito
Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus na Adams Oshiomhole ya fito
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

A wani rahoton, mun kawo muku cewa shugaban hukumar kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari ya sanar da cewa hukumar mai kula da man fetur da iskar gas za ta bayar da gudunmawar dallar Amurka miliyan 30 kimanin Naira biliyan 11,093,719,460.80 ga gwamnatin Najeriya domin yaki da annobar coronavirus a kasar.

Kyari ya yi wannan jawabin ne a babban birnin tarayya Abuja a wurin taron manema labarai da ake gudarwa a halin yanzu kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Ya ce, "Muna sanar da cewa a karo na farko za mu bayar da kudi dallar miliyan 30 a matsayin tallafi domin yaki da kayar cutar Covid-19 a Najeriya.

"Wannan gudunmawar za a bayar da shi ne ga gwamnatin tarayya a yunkurin da ta ke yi na takaita yaduwa da kawo karshen annobar Covid-19 a kasar.

"Da wannan gudunmar da ma'aikatar ta bayar, za mu samar da kayan aikin asibiti, zirga-zirga da tallafawa masu jinya da kuma samar da kayayyakin da asibitoci ke bukata da za a dade ana amfani da su a kasar."

Tuni dai wasu attijarai a Najeriya suma sun yi hubbasa wurin bayar da gudunmawar kudi domin taimakawa gwamnati yaki da cutar ta Covid-19. Wasu daga cikin wadanda suka bayar da tallafin sun hada da Alhaji Aliko Dangote, Femi Otedola, Tony Elemulu da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel