Yanzu-yanzu: Mutane 5 sun sake kamuwa da Coronavirus, 3 a Abuja, 2 a Oyo - 70 jimilla

Yanzu-yanzu: Mutane 5 sun sake kamuwa da Coronavirus, 3 a Abuja, 2 a Oyo - 70 jimilla

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane biyar da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Talata inda tace: “An tabbatar da mutane biyu sun kamu da #COVID19 a Najerya. 3 a Abuja, biyu a Oyo.“

“Misalin karfe 8 na ranar 27 ga Maris, an samu mutane 70 da aka tabbatar sun kami da COVID19 a Najeriya, an sallami uku, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“

Ge jerin bullar a jihohi

Lagos- 44

Abuja- 14

Ogun- 3

Ekiti- 1

Oyo- 3

Edo- 1

Bauchi- 2

Osun-1

Rivers-1

KU KARANTA Covid-19: Akwai yiwuwar mutum 39,000 su kamu da cutar a Legas - Kwamishinan Lafiya

Mun kawo muku rahoton cewa Kasar Italiya ta waye gari yau Jumaa cikin bakin ciki da radadi sakamakon mutuwar mutane 969 sakamakon cutar Coronavirus, adadi mafi yawa a duniya tun barkewar cutar.

Amma adadin masu kamuwa da cutar ta ragu a yau, yayinda hukumar hana yaduwar cutar kasar ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 86,500 suka kamu da cutar - ta biyu bayan kasar Amurka mai sama da 100,000. Kawo yanzu mutane 558,905 sun kamu da cutar.

Yayinda mutane 127,709 sun warke, 25,251 sun rigamu gidan gaskiya. A ranar Jumaa, an bayyana Amurka matsayin hedkwatar Coronavirus a duniya yayinda ta zarcewa Italiya matsayin kasa mafi yawan masu dauke da cutar.

Har yanzu, masanin kimiya na cigaba da bincike kan neman rigakafin cutar da kuma maganinta amma basu cimma ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel