COVID-19: FG ta bada umarnin sakin kashi 70 cikin 100 na 'yan gidan gyaran hali
Matakan hana yaduwar muguwar cutar coronavirus da gwamnatin tarayya ke dauka a kasar nan suna da yawa ,kuma a halin yanzu har sun kai gidajen gyaran hali. A cikin wannan kokarin ne gwamnati ta bada umarnin cewa a saki wadanda ake kan shari'arsu amma ake garkame dasu a gidajen.
Kamar yadda ministan lamurran cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana, an yi hakan ne don hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali.
Aregbesola ya bada wannan umarnin ne a yayin wani taron gaggawa da ya kira a ofishinsa a Abuja a kan yadda za a hana yaduwar cutar a gidajen gyaran hali.
Bayan taron ne ministan ya fitar da takarda wacce aka mika ga manema labarai ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama'a, Mohammed Manga, inda ya ce wannan umarnin ya biyo bayan hukuncin kwamitin fadar shugaban kasa na yakar cutar ne.
Ya kara da cewa an dauka matakan ne don kare masu zama a gidajen gyaran halin, ma'aikatansu da kuma sauran 'yan Najeriya.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: COVID-19: Mu sadaukar da albashinmu na watan Maris - Dan majalisar wakilai
Aregbesola, wanda ya jaddada cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali wanda ke bukatar hadin kai kowa don tabbatar da cewa cutar ba ta yadu ba, ya ce ba za su zuba wa gidajen gyaran halin ido ba.
Ya yi kira ga Antoni Janar kuma ministan shari'ar kasar nan, manyan alkalan jihohi, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren shari'a da su dauka matakan gaggawa don tabbatar da cewa an rage yawan jama'ar da ke dankare a gidajen gyaran halin kasar nan.
Kamar yadda yace, yawan wadanda ke cikin gidajen gyaran halin sun yi yawa kuma duba da halin da kasar nan ke ciki, akwai yuwuwar in cutar ta shiga tayi barna.
Ya kara da cewa akwai jama'a da yawa da ke gidan amma suna jiran kammalar shari'arsu, wadanda sune suka kunshi kashi 70 na wadanda ke gidan.
Ya yi kiran gaggawa a kan hakan tare da bukatar a kawo hanyar da za a shawo kan wannan kalubalen.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng