An rufe majalisar jihar Zamfara saboda fargabar Coronavirus

An rufe majalisar jihar Zamfara saboda fargabar Coronavirus

Majalisar Jihar Zamfara ta sanar da dakatar da zamanta da sauran ayyukan ta har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Kakakin majalisar, Honarabul Nasiru Magarya ne ya bayyana hakan cikin wata sako da ya aike wa manema labarai a Gusau a ranar Alhamis ta hannun jami'in hulda da jama'a na majalisar Mustafa Jafaru Kaura.

Mista Margaya ya bayyana matukar damuwarsa a kan yadda mummunar cutar ta Coronavirus ta zama annoba ga duniya baki daya.

Ya kuma ce majalisar ta soke dukkan wasu ayyukan ta ciki har da zaman majalisa, zaman kwamitoci da ayyukansu na sa ido duk a matsayin wani mataki na kare yaduwar cutar a jihar.

An rufe majalisar jihar Zamfara saboda fargabar Coronavirus
An rufe majalisar jihar Zamfara saboda fargabar Coronavirus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa

Kakakin majalisar ya ce, "ba a samu bullar cutar a jihar ba amma sun san irin kokarin da hukumomin da abin ya shafa su ke yi domin tabbatar da cewa cutar bai shigo jihar mu ba.

"Muna yabawa kokarin da gwamna Bello Matawalle ya ke yi domin ganin an kare yaduwar cutar a jihohin Arewa 19.

"Sakamakon wannan matakin na dakatar da aiki, muna umurtar dukkan 'yan majalisa su zaune a gidajensu har zuwa wani lokaci nan gaba."

A wani rahoton kun ji cewa ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce akwai yiwuwar za a iya yada kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus ta hanyar jima'i.

Yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Mista Ehanire ya ce ya yi imanin cewa "idan mutum yana dauke da kwayar cutar ta coronavirsu, zai iya yada wa ta hanyar jima'i."

Sai dai a akwai bukatar da ayi amfani da kimiyya wurin gwaji domin tabbatar da hakan duba da cewa Covid-19 sabon cuta ne kuma har yanzu ana cigaba da bincike domin gano hanyoyin yaduwar cutar.

Wasu masu binciken kimiyya sun yi ikirarin cewa ba za a iya yada kwayar cutar da hanyar jima'i ba sai dai kawai ta bakin mutum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel