Annobar Coronavirus: Dakarun Sojin Najeriya a shirye suke su garkame Najeriya

Annobar Coronavirus: Dakarun Sojin Najeriya a shirye suke su garkame Najeriya

Kafatanin rundunonin Najeriya na zaune cikin shirin ko-ta-kwana tare da aiki da cikawa domin dabbaka umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na garkame Najeriya da zarar ya bayar da umarnin yin hakan sakamakon yaduwar annobar Coronavirus.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata majiya daga cikin manyan jami’an Sojin kasar nan ta shaida mata cewa an aika ma kowanne rukunin Sojin Najeriya sako daga shelkwatar tsaro ta kasa a kan su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, a ranar Talata.

KU KARANTA: Ana wata ga wata: An yi garkuwa da Yayan gwamnan Bauchi kwana daya da kamuwarsa da Corona

Haka zalika wasu kafafen sadarwa na yanar gizo sun wallafa wasu takardu da suka yi ikirarin sun fito ne daga shelkwatar tsaro ta kasa dake bayyana shirin Sojoji na mamaye kasar cikin kankanin lokaci domin tabbatar da jama’a kowa ya zauna a gidansa don kauce ma yaduwar annobar.

Wannan rahoto ya fito ne bayan kimanin sa’o’i 72 da ministan watsa labaru, Lai Muhammad ya bayyana cewa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don kare yaduwar cutar ta bashi shawarar daukan wasu tsauraran matakai.

Haka zalika majiyar ta mu ta bayyana cewa an umarci manyan kwamandojin Sojin Najeriya su fara horas da Sojojinsu don shirin wannan muhimmin aiki. “Za’a gudanar da horon ne tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro don cimma manufar garkame kasar.” Inji majiyar.

A yanzu haka a cewar majiyar, an tsara yadda za’a samu manyan motocin dauka kaya domin kwashe gawarwakin jama’a idan har aikin garkame kasar ta kai ga mutuwar wasu, ko kuma na wadanda suka suka mutu a sanadiyyar cutar.

Sai dai kwararru a harkar tsaro sun nuna rashin amincewa da daukan wannan mataki, daga cikinsu akwai Ambrose Aisabor, tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, wanda yace wannan ba aikin Sojoji bane, kamata yayi a sanya Yansanda a kan gaba wajen aikin idan har ta kama.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da shirinta na garkame jahar Kano gaba daya ta hanyar rufe duk wata hanya da ta shiga jahar daga sauran makwabta jahohi.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a kokarin na yaki da yaduwar mugunyar cutar nan mai toshe numfashi, watau annobar Coronavirus, kamar yadda hadimin gwamnan na musamman a kan harkokin kafafen watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel