Da duminsa: Gwamnan Ekiti ya killace kansa bayan haduwa da mutane 2 masu cutar Coronavirus

Da duminsa: Gwamnan Ekiti ya killace kansa bayan haduwa da mutane 2 masu cutar Coronavirus

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa ya shiga killace kansa na tsawon makonni biyu bayan haduwa da mutane biyu da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Coronavirus.

Gwamnan ya bayyana hakan ne shafinsa na Tuwita a ranar Laraba, 25 ga watan Maris, 2020.

Yace “Yanzu aka yi min gwajin cutar COVID19 bayan na killace kaina tun yammacin jiya. Ina cikin koshin lafiya, amma na zauna da mutane biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar.“

“Ina kyautata zaton ban kamu ba kuma na yi kira ga dukkan takwarai na suyi gwaji.“

Da duminsa: Gwamnan Ekiti ya killace kansa bayan haduwa da mutane 2 masu cutar Coronavirus

Da duminsa: Gwamnan Ekiti
Source: Depositphotos

A bangare guda, Ta tabbata kakakin majalisar dokokin jihar Edi, Frank Okiye, ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar Edo, mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya laburta a Benin City.

Kakakin ya yi tafiya zuwa kasar Ingila kuma ya killace kansa daga dawowa a asibitin Irrua, dake karamar hukumar Esan na jihar.

Ya kara da cewa mutane biyu da ake zargin sun hadu da kaakakin sune matarsa da yarinyarsa kuma an gwada su, basu kamu ba.

Phiilip Shaibu yace “Ya tura samfurin jininsa kuma sakamakon shine ya kamu. Yana cikin koshin lafiya kuma sakamakon gwain da akayi iyalansa ya nuna cewa basu kamu ba.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel