Gwamna Lalong ya bayar da umurnin rufe kasuwanni, ya ce ma'aikata suyi aiki daga gidajensu

Gwamna Lalong ya bayar da umurnin rufe kasuwanni, ya ce ma'aikata suyi aiki daga gidajensu

Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya bayar da umurnin ma'aikatan gwamnati masu mataki na daya zuwa 12 a jihar su fara yin aiki daga gidajensu sannan kuma a rufe kasuwanni.

Dokar za ta fara aiki daga ranar Laraba 25 ga watan Maris kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

An dauki matakin ne yayin taron gaggawa da majalisar zartarwa na jihar ta yi domin kare yaduwar annobar kwayar cutar Covid-19 da ke kisa ba kakautawa.

Gwamnan ya ce, "Daga ranar Laraba 25 ga watan Maris na 2020, dukkan ma'aikatan gwamnati a jihar Plateau daga mataki na 12 zuwa daya za su fara aikin daga gidajensu na tsawon kwanaki 30.

Gwamna Lalong ya bayar da umurnin rufe kasuwanni, ya ce ma'aikata suyi aiki daga gidajensu
Gwamna Lalong ya bayar da umurnin rufe kasuwanni, ya ce ma'aikata suyi aiki daga gidajensu
Asali: Twitter

"Kawai ma'aikata da ke yin ayyukan da ake bukatarsu sosai kamar tsaro, lafiya, kafafen yada labarai, masu sharar titi, samar da ruwa da lantarki ne wannan dokar ba ta shafa ba.

"Domin hakan, gwamnati tana umurtar dukkan kasuwanni su rufe daga ranar 25 ga watan Maris na 2020. 'Yan kasuwa da ke sayar da kayan abinci, magunguna da iskar gas na girki ne kawai wannan dokar ba ta shafa ba.

"Bugu da kari an hana sayar da kayayyaki a titi da barace-barace. Kasuwanni na ranar Lahadi da ke Ahmadu Bello Way, Bukuru da wuraren da ke kusanci da su suma an rufe su," in ji gwamnan.

Dokar kuma ta ce dukkan masu wuraren shakatawa kamar kulob da mashaya su ma su rufe daga ranar 25 ga wtaan Maris na 2020. Masu sayar da abinci kuma su rika kai wa kwastomominsu abincin gida domin hana cinkoso.

Gwamna Lalong ya kuma ce za a rika yi wa dukkan mutanen da za su shigo jihar gwaji domin tabbatar da cewa ba su da alamun cutar.

Gwamnan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana saba dokokin sai fuskanci fushin hukuma duba da cewa an bawa hukumomin tsaro umurnin su dauki mataki a kansa.

Ya ce, "Idan har lamarin ya cigaba a haka, ba za mu yi wata-wata ba wurin rufe dukkan harkoki a jihar domin tsare rayukar al'ummar mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel