COVID-19: Gwamnan Bauchi ya aike sako ga jama'ar jiharsa bayan tabbacin yana da cutar

COVID-19: Gwamnan Bauchi ya aike sako ga jama'ar jiharsa bayan tabbacin yana da cutar

Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya bukaci jama'ar jiharsa da kada su ji tsoro a kan kebancesa da aka yi sakamakon cutar coronavirus da ya kamu da ita.

A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa gwamnan na dauke da cutar coronavirus din.

Mohammed ya killace kansa tun bayan da yayi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, wanda aka gano yana dauke da cutar, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, Mohammed ya ce yana lafiya kuma har yanzu bai fara nuna wata alama ta cutar ba.

"Kamar yadda zai yuwu kun sani, an gano ina dauke da coronavirus," Mohammed yace.

"Tuni na killace kaina na kwanakin da suka gabata kuma har yanzu ina kebance har sai na samu tabbaci daga likitoci cewa zan iya ci gaba da mu'amala da jama'a. Ina lafiya kuma ban fara nuna wata alamar cutar ba. Ina kira ga kowa da ya kwantar da hankali kuma kada a firgita. Za mu tsallake." yace.

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutane 44 ne a kasar nan suka kamu da cutar.

A cikin 44 ne aka samu 29 a jihar Legas, 8 a Abuja, 3 a Ogun, Ekiti, Oyo, Edo da Bauchi duk mutane dai-daya.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya nada yaro mai shekaru 15 a matsayin sarki mai daraja ta daya a jiharsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel