Coronavirus: Majalisar Malaman Kaduna ta dakatad da Sallar Juma'a da Khamus-Salawati
Majalisar Malamai da Limaman jihar Kaduna sun bukaci dakatad da Sallar Juma'a da Khamsu-Salawati idan mamu sun zarce mutane 20 a fadin jihar saboda annobar COVID-19.
Sakatare Janar na majalisar, Malam Yusuf Arrigasiyyu, a jawabin da ya sake ranar Talata a Kaduna, ya shawarci dukkan Masallatan Juma'a su dakatar.
A cewarsa “Muna bada shawaran cewa dukkan Masallatan Juma“a da Khamsu-Salawati da adadin mamu ya zarce 20 su dakatar har sai lokacin da aka sanar a bude.“
“Majalisar ta jaddada cewa sun dau wannan mataki ne bisa ga koyarwan Manzon Allah (SAW).“
“Hakazalika muna kira ga mutan jihar Kaduna su bi umurnin likitoci a koda yaushe kuma su guji yada cutar coronavirus.“
Arrigasiyu ya jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna kan matakan da ta dauka wajen hana shigowar cutar jihar Kaduna.
Majalisar ta yi kira ga mutane su taimakawa makwabtansu da wannan kulle zai shafa musamman bangaren kayan abinci da rayuwar yau da kullum.
Ya bukaci yan uwa Musulmai su kasance cikin addua da kai dauki wajen Allah don kawar mana da wannan cutar.

Asali: Facebook
KU KARANTA Ma'aikatan Aso Villa 3 sun kamu da cutar Coronavirus
A bangare guda, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayar da umurnin rufe kasuwannin da ke jihar banda wadanda ake sayar da kayan abinci da magunguna.
Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne yayin wata taron manema labarai a kan Covid-19 wato Coronavirus a ranar Talata.
Ya ce ba zai yi wu a rufe dukkan kasuwanci ba a Legas saboda irin abinda zai faru da tattalin arzikin jihar amma za a dauki dukkan matakan da suka dace domin hana yaduwar cutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng