Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2, 1 a Legas, 1 a Ogun - 42 kenan

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2, 1 a Legas, 1 a Ogun - 42 kenan

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane biyu da suka kamu da cutar Coronavirus (COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Talata inda tace: “An tabbatar da mutane biyu sun kamu da #COVID19 a Najerya. 1 a Legas, daya a Ogun.“

“Misalin karfe 1 na ranar 24 ga Maris, an samu mutane 42 da aka tabbatar sun kami da COVID19 a Najeriya, an sallami biyu, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“

A cewar NCDC, daya matafiyi ne da ya dawo Najeriya, dayan kuma ya kama ne daga jikin wani.

Gajerin halin da ake ciki

Lagos- 29

FCT- 7

Ogun- 3

Ekiti- 1

Oyo- 1

Edo- 1

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2, 1 a Legas, 1 a Ogun - 42 kenan

An samu karin masu cutar Coronavirus 2, 1 a Legas, 1 a Ogun - 42 kenan
Source: Facebook

A bangare guda, Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta hana ganin shugaban kasa bayan an gano cewa shugaban ma'aikatan fadarsa, Abba Kyari na dauke da mugunyar cutar Coronavirus.

Idan zamu tuna, wasu sassan na kafofin yada labarai sun ruwaito cewa Kyari na dauke da cutar COVID-19. Amma kuma, a ranar Litinin an gano cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya dauke da cutar kamar yadda NCDC ta bayyana.

Kamar yadda rahoton da jaridar Thisday ta ruwaito ya bayyana, akwai yuwuwar Kyari ya kamu da cutar ne bayan da ya kai ziyara kasar Jamus a ranar Asabar, 7 ga watan Maris don taro da jami'an kamfanin Siemens a Munich.

A don haka ne uwargidan shugaban kasar ta saka masa dokar zaman gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel