Cikin hotuna: Yadda jama'a ke rububin sayen kayan kare kai daga kamuwa da kwayar cutar coronavirus a Legas

Cikin hotuna: Yadda jama'a ke rububin sayen kayan kare kai daga kamuwa da kwayar cutar coronavirus a Legas

A ranar Talata ne mazauna jihar legas suke ta tururuwar zuwa siyan takunkumin fuska da safar hannu a kasuwa don kare kai daga kamuwa da mugunyar cutar coronavirus.

Idan zamu tuna, ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ya yi barazanar sakin sunayen wadanda suka ki bin dokar killace kansu don taimakawa hana yada cutar a kasar nan.

Ehanire ya bada wannan sanarwar ne a ranar Litinin a Abuja yayin zantawa da manema labarai a kan halin da kasar nan ke cikin a kan annobar Covid-19.

"Muna sanar da wasu jama'a da su killace kansu na kwanaki 14 don hana yaduwar cutar nan. Killace kai na daga cikin matakin kare mutane da ke tare da kai, iyalai da kuma abokai daga samun cutar. Abin yin shine, amfani da hanklai wajen daina mu'amala da jama'a ta duk yadda ya dace," yace.

Cikin hotuna: Yadda jama'a ke rububin sayen kayan kare kai daga kamuwa daga kwayar cutar coronavirus a Legas
Cikin hotuna: Yadda jama'a ke rububin sayen kayan kare kai daga kamuwa daga kwayar cutar coronavirus a Legas
Asali: Twitter

Ministan yayi kira ga 'yan Najeriya da su dage da killace kansu tare da nisantar juna. Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta tilastawa 'yan kasa killace kansu ba kamar yadda wasu kasashen duniya suka yi ba.

DUBA WANNAN: COVID 19: Ministan lafiya ya yi barazanar bayyana sunayen manyan da suka ki yarda a gwada su

Cikin hotuna: Yadda jama'a ke rububin sayen kayan kare kai daga kamuwa daga kwayar cutar coronavirus a Legas
Cikin hotuna: Yadda jama'a ke rububin sayen kayan kare kai daga kamuwa daga kwayar cutar coronavirus a Legas
Asali: Twitter

Minsitan ya ce gwamnati za ta dogara da yadda ta ga 'yan Najeriya sun dau matakan kiyaye kai daga cutar ne ballantana wadanda suka dawo daga kasashen da cutar tayi kamari.

"Za mu ci gaba da rokon wadanda suka fita daga Najeriya a kwanaki 14 da suka gabata da su sanar ta yadda ba za mu takura tsarin ma'aikatun lafiyarmu ba," yace.

Amma kuma, ministan ya sanar da cewa kasar nan na ci gaba da samun tallafi da gudumuwa daga abokanta da kawayenta. Ya ce gwamnati za ta yi aiki tare da hadin guiwar asibitoci masu zaman kansu don karfafa bincike a kan cutar.

Ehanire ya ce ma'aikatar lafiya, ta hannun cibiyar kula da yaduwar cutuka (NCDC) za ta yi aiki tare da duk gwamnatocin jihohin da abin ya shafa don zakulo wadanda suka yi cudanya da masu cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel