Coronavirus: Adadin mutanen da suka kamu ya kai 40 - 3 a Legas, 1 a Abuja

Coronavirus: Adadin mutanen da suka kamu ya kai 40 - 3 a Legas, 1 a Abuja

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane hudu da suka kamu da cutar Coronavirus (COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita da daren Litinin inda tace: “An tabbatar da mutane hudu sun kamu da #COVID19 a Najerya. 3 a Legas, daya a birnin tarayya.“

A wani labarin mai alaka, Ma'aikatar kiwon lafiyar Najeriya ta yi kira fa gwamnatin kasar Sin ta kawowa Najeriya dauki wajen yakar cutar Coronavirus a kasar bayan an samu mutane akalla 36 kuma daya ya mutu.

Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya mika wannan bukata ne yayinda jakadan kasar China zuwa Najerieya, Zhou Pingjian, ya kawo gudunmuwar kayayyakin aiki da magunguna ma'aikatar ranar Litinin a Abuja.

Ehanire ya yabawa gwamnatin kasar Sin kan namijin kokarin da sukayi wajen kawar da cutar a kasarsu yayinda mutane da al'ummar kasar suka koma rayuwarsu kamar bai faru ba.

Ya ce hanyoyin da kasar Sin tayi amfani da su wajen kawo karshen cutar zai zama abin koyi ga Najeriya wajen yakarta.

Saboda haka ya yi kira da gwamnatin kasar Sin ta taimakawa Najeriya da ma'aikata da zasu taimaka wajen shawo kan lamarin.

Ya ce Najeriya na bukatar daukar karatu wajen gwamnatin Sin kan yadda ta takaita yaduwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel