Yadda aka tsananta duba lafiyar baki a fadar shugaban kasa

Yadda aka tsananta duba lafiyar baki a fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasar Najeriya ta tsananta tantance lafiyar baki da ma'aikata a gidan gwamnati da ke Abuja a matsayin hanyar kariya daga annobar coronavirus

- An ga ma'aikatan lafiyar da ke wajen tarbar baki a fadar shugaban kasar a jiya duk sun saka takunkumin fuska

- Ma'aikatan lafiyar na ta amfani da na'urar gwajin dumin jikin jama'a wacce ke iya bayyana dumin jikin dan Adam a take don tantancewa ga baki da kuma ma'aikata

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tsananta tantance lafiyar baki da ma'aikata a gidan gwamnati da ke Abuja a matsayin hanyar kariya daga annobar coronavirus. Ma'aikatan lafiyar da ke wajen tarbar baki a fadar shugaban kasar a jiya duk sun saka takunkumin fuska.

Ma'aikatan lafiyar na ta amfani da na'urar gwajin dumin jikin jama'a wacce ke iya bayyana dumin jikin dan Adam a take don tantancewa ga baki da kuma ma'aikata.

An samar da sinadarin kashe kwayoyin cuta don amfanin hannu a fadar.

Yadda aka tsananta duba lafiyar baki a fadar shugaban kasa
Yadda aka tsananta duba lafiyar baki a fadar shugaban kasa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna a kasuwa

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta dauki babban mataki domin kare yaduwar annobar kwayar cutar coronavirus bayan ta umarci dukkan ma'aikatanta daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida na tsawon kwanaki 30 masu zuwa. Umranin zai fara aiki ne daga ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kazalika, gwamnatin ta umarci duk wasu 'yan kasuwa su rufe shagunansu. Masu shagon sayar da magani da kayan abinci kadai aka yarda su bude shagunansu a jihar.

A cikin jerin wasu sakonni da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da jami'an tsaro wajen tabbatar da cewa an yi wa dokar hana jama'a da yawa taruwa a wuri guda biyayya, musamman a coci-coci, masallatai da kuma makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da ma na addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel