COVID 19: Ministan lafiya ya yi barazanar bayyana sunayen manyan da suka ki yarda a gwada su

COVID 19: Ministan lafiya ya yi barazanar bayyana sunayen manyan da suka ki yarda a gwada su

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ya yi barazanar sakin sunayen wadanda suka ki bin dokar killace kansu don taimakawa hana yada cutar a kasar nan.

Ehanire ya bada wannan sanarwar ne a ranar Litinin a Abuja yayin zantawa da manema labarai a kan halin da kasar nan ke cikin a kan annobar Covid-19.

"Muna sanar da wasu jama'a da su killace kansu na kwanaki 14 don hana yaduwar cutar nan. Killace kai na daga cikin matakin kare mutane da ke tare da kai, iyalai da kuma abokai daga samun cutar. Abin yin shine, amfani da hanklai wajen daina mu'amala da jama'a ta duk yadda ya dace," yace.

Ministan yayi kira ga 'yan Najeriya da su dage da killace kansu tare da nisantar juna. Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta tilastawa 'yan kasa killace kansu ba kamar yadda wasu kasashen duniya suka yi ba.

Minsitan ya ce gwamnati za ta dogara da yadda ta ga 'yan Najeriya sun dau matakan kiyaye kai daga cutar ne ballantana wadanda suka dawo daga kasashen da cutar tayi kamari.

"Za mu ci gaba da rokon wadanda suka fita daga Najeriya a kwanaki 14 da suka gabata da su sanar ta yadda ba za mu takura tsarin ma'aikatun lafiyarmu ba," yace.

COVID 19: Ministan lafiya ya yi barazanar bayyana sunayen manyan da suka ki yarda a gwada su
COVID 19: Ministan lafiya ya yi barazanar bayyana sunayen manyan da suka ki yarda a gwada su
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna a kasuwa

Amma kuma, ministan ya sanar da cewa kasar nan na ci gaba da samun tallafi da gudumuwa daga abokanta da kawayenta.

Ya ce gwamnati za ta yi aiki tare da hadin guiwar asibitoci masu zaman kansu don karfafa bincike a kan cutar.

Ehanire ya ce ma'aikatar lafiya, ta hannun cibiyar kula da yaduwar cutuka (NCDC) za ta yi aiki tare da duk gwamnatocin jihohin da abin ya shafa don zakulo wadanda suka yi cudanya da masu cutar.

"Ta hanyar zakulo wadanda suka yi wata mu'amala da masu cutar wanda NCDC ke yi, muna ta gano masu cutar da wuri. Ina kira ga cibiyoyin lafiya da su kasance a shirye; muna son gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da su kasance masu tabbatar da an bi doka tare da hadin guiwar shugabannin gargajiya," yayi kira.

Ya kara da cewa gwamnati na kokarin karo naurorin taimakon numfashi kuma nan ba da dadewa ba za a gina dakin binciken cutuka na tarayya yadda za a samu guda shida a fadin kasar nan da ke iya gane cutar.

Ya kara da cewa, likitoci da ma'aikatan jinya masu murabus duk za a kirasu don bukatar aikinsu idan hakan ta kama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng