Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2 a Abuja, 2 a Legas, 1 a Edo

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2 a Abuja, 2 a Legas, 1 a Edo

Labarin da duminsa na nuna cewa an smau karin masu cutar Coronavirus biyar a Najeriya da safiyar yau Litinin, 23 ga Maris, 2020. Cibiyar NCDC ta tabbatar.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita da safiyar Litinin, 23 ga Mairs misalin karfe 09:45 am.

Jawabin yace “An tabbatar da mutane biyar da suka kamu da COVID19: 2 in Abuja, 2 a Lagos & 1 a Edo. 2 sun dawo daga kasar Ingila.“

A yanzu ga adadin masu cutar a jihohi

Lagos- 24

FCT- 6

Ogun- 2

Ekiti- 1

Oyo- 1

Edo- 1

Jimilla: 35

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2 a Abuja, 2 a Legas, 1 a Edo
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 2 a Abuja, 2 a Legas, 1 a Edo
Asali: Twitter

A bangare guda, Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, a zaben 2019 Atiku Abubakar ya sanar da cewa ɗan sa ya kamu da ƙwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus.

Atiku ya sanar da hakan ne a shafinsa na dandalin sanda zumunta na Twitter a ranar Lahadi 22 ga watan Maris na 2020.

Ya rubuta, "Da na ya kamu da ƙwayar cutar Coronavirus."

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya, an garzaya da dan sa zuwa asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja domin yi masa magani.

Ya kara da cewa, "An sanar da hukumar kula da Cututtuka masu saurin yaduwa ta Najeriya @NCDCGov kuma an kai shi asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a Abuja domin yi masa magani da kulawa da shi.

Zan yi farin ciki idan za ku iya saka shi a addu'o'in ku. Ku cigaba da kiyaye wa domin Coronavirus gaskiya ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel