Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 10 a Najeriya, 3 a Abuja
Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu karin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Asabar, 21 ga watan Maris, 2020.
Yayinda bakwai aka samu a Legas, sauran ukun na birnin tarayya Abuja.
Yanzu dai akwai jimillar masu cutar 22 a Najeriya kuma an sallami biyu da suka samu sauki.

Asali: Facebook
Yace “Najeriya ta samu sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar Coronavirus a Legas da Abuja. A yanzu haka akwai jimillar mutane 22 a Najeriya: Lagos 16, FCT 3, Ekiti 1 da Ogun 2.An sallami biyu.“
“Dukkansu yan Najeriya ne, 9 sun dawo daga kasar Faransa, Holan, Kanada, Spain da Ingila, daya ya kwasa ne daga wani daga cikinsu.“
“Wadanda ke Abuja ana jinyarsu a asibitin koyarwan jamiar UNIABUJA.“
“Wadanda ke Legas kuma ana jinyarsy a asibitin cututtuka a Legas.“
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng