Abinda na gani a sansanin 'yan gudun hijira ya firgita ni - Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abinda ya gani a sansanin 'yan gudun hijira da 'yan Boko Haram suka fatattaka
- Yace ya ga abubuwan tashin hankali da alhini saboda haka ne yasa ba zai iya komawa can ba
- Buhari ya ce ya ga yara kanana da basu san iyayensu ba balle su san daga inda suka fito
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana abinda ya gani a sansanin 'yan gudun hijira da 'yan Boko Haram suka fatattaka. Yace ya ga abubuwan tashin hankali da alhini saboda haka ne yasa ba zai iya komawa can ba.
Buhari ya ce ya ga yara kanana da basu san iyayensu ba balle su san daga inda suka fito, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.
Yace bayan Danjuma, tsohon shugaban tsaro kuma biloniya a yanzu ya ce ba zai iya daukar mukamin da ya bashi ba saboda yawan shekarunsa, ya yanke shawarar kafa ma'aikata guda da za ta dinga kula da lamurran jin dadi da walwalar 'yan kasa.
"Na je sansani uku kacal amma tun daga nan ban iya komawa ba saboda ba zan iya jure ganin halin da suke ciki ba," shugaban kasar yace.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Coronavirus: Diyar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga kasar waje
Ya yi wannan maganar ne a Abuja yayin rantsar da kwamitin ayyuka na jin kai da walwalar 'yan kasa.
"Domin karin haske, ina son yin tsokaci a kan ziyarar da na kai sansanin 'yan gudun hijira. Gaskiya mummunan lamarin da na gani ne yasa na bukaci daya daga cikin manyan sojin da muke dashi, Janar T.Y Danjuma a kan ya shugabanci ma'aikatar.
"Saboda abinda muke samu daga kungiyoyin taimakon kai da kai baya zuwa inda ya dace. Idan ka ga yara, basu san iyayensu ba ballantana inda suka fito. Na so ya shugabanci wajen don su samu kulawa mai inganci.
"Sansani uku na ziyarta amma na kasa komawa saboda ba zan iya jure ganin mummunan lamarin ba," shugaban kasar yace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng