Da duminsa: Bayan watanni 3 a rabon da ya taka jiharsa, Gwamnan Taraba zai koma gida yau

Da duminsa: Bayan watanni 3 a rabon da ya taka jiharsa, Gwamnan Taraba zai koma gida yau

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku zai koma gida ranar Alhamis bayan kwashe kwanaki 87 rabonsa da taka jihar da yake jagoranta ba tare da baiwa mataimakinsa rikon kwarya ba. The Nation ta ruwaito.

Kwamishanan yada labaran jihar, Danjuma Adamu, wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa mutan jihar na cikin shewa domin tarbar gwamnan.

Hakazalika, mambobin jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP), da yan majalisar zartarwar jihar sun kafa kwamiti na musamman domin tarbar gwamnan.

An sa ran gwamnan zai sauka a filin jirgin saman Danbaba Suntai misalin karfe 4 na yamma.

Masoya gwamnan da abokan arziki sun sanya jajayen kaya na musamman domin tarbarsa.

Da duminsa: Bayan watanni 3 a rabon da ya taka jiharsa, Gwamnan Taraba zai koma gida yau
Gwamnan Taraba zai koma gida yau
Asali: UGC

A baya mun kawo muku rahoton cewa Aikin shi na karshe kafin barin jihar shine gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2019.

Jim kadan bayan gabatarwar, aka samu rahoton cewa ya bar Jalingo a ranar 22 ga watan Disamba 2019 kuma tun daga nan ba’a sake ganin kafarsa ba.

Gwamnan bai bar wa mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu, rikon kwarya ba, sannan bai sanarwa yan majalisar jihar ba.

KU KARANTA: Sanatan YPP daya tilo ya tsallake rijiya da baya, kotu ta tabbatar da shi

Bincike ya nuna cewa tun daga 19 ga watan disamba 2019 har yau, ba’a sake ganawar majalissar zantarwar jihar ba.

Har ila yau, ba wani aiki da yake gudana yanzu a Jalingo, mutane da yawa na jihar sun nuna damuwar su game da rashin gwamnan.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Barista Ibrahim EL-sudi, yace rashin gwamnan a jihar har na kimanin kwanaki 55 ba tare da wani dalili ko ba mataimakin shi rikon kwarya ba babban kuskure ne.

Yace “Bama cikin farin ciki saboda rashin gwamna domin akwai abubuwan da mataimakin shi ba zai iya yi ba idan baya nan, aiyuka da dama sun tsaya cak a jihar.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel