Gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur zuwa N130

Gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur zuwa N130

Jaridar The Nation ta rawaito cewa alamu na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da rage farashin litar man fetur zuwa N125 daga tsohon farashinsa, N145.

A cewar 'The Nation', majiyarta a fadar shugaban kasa ta sanar da ita cewa shugaba Buhari zai amince da bukatar rage kudin farashin litar man bayan karamin ministan man fetur na kasa, Timipre Sylva, ya gabatar da bukatar neman yin hakan yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da ake yi duk sati a fadar shugaban kasa.

A cewar majiyar, wacce bata amince a ambaci sunanta ba, Sylva ya gabatar da bukatar rage farashin litar man fetur din ne biyo bayan zabgewar farashin danyen man fetut a kasuwar duniya.

Sai dai, duk da jaridu sun bayyana hakan, babu wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasa ko ofishin karamin ministan a kan rage farashin litar man fetur din saboda har yanzu ba a kammala taron ba lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur zuwa N130
Gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur zuwa N130
Asali: UGC

A wani labari na daban, a yau Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a jihar Kano ta saka ranar 23 ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar da tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya mika a gabanta na bukatar ta dakatar da hukumar korafi da yaki da rashawa ta jihar a kan bincikarsa.

DUBA WANNAN: Zargin badakala: Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron korafin tsohon sarki Sanusi II

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Sanusi ya mika bukatar ne gaban kotun a kan ta dakatar da shugaban PCACC, Muhyi Rimingado, Antoni janar din jihar Kano da Gwamna Abdullahi Ganduje daga bincikarsa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyan ya ruwaito cewa, a ranar 6 ga watan Maris ne kotun ta dakatar da PCACC a kan bincikar Sanusi tare da bukatarta da ta tsaya har sai an ci gaba da sauraron shari'ar.

Wadanda ake karar sun hada da hukumar korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Rimingado, Antoni janar din jihar Kano da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel