Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, ya jagoranci Sallar Jumaa a Awe (Hotuna)

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, ya jagoranci Sallar Jumaa a Awe (Hotuna)

Tubabben Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya jagoranci Sallar Jumaa yau a babbar Masallacin Awe, dake karamar hukumar Awe, jihar Nasarawa idan aka kaishi.

A bangare guda, Babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga inda aka tsare shi a garin Awe na jihar Nasarawa bayan an cire daga kan mulki a ranar Litinin.

Mai shari'ar Anwuli Chikere ne ta bayar da umurnin sakamakon bukatar da shugaban lauyoyinsa, Latee Fagbemi (SAN) ya shigar a ranar Juma'a.

Kotun ta ce a mika takardan umurnin sakin Sanusi da dukkan hukumomin da suka tsare da shi.

Wadanda Sanusi ya yi karar su a kotun kan batun tsare shi suna hada da Sifeta Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi; Attony Janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da Ministan Shari'a na Najeriya, Mista Abubakar Malami (SAN).

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, ya jagoranci Sallar Jumaa a Awe (Hotuna)
Tsohon Sarkin Kano, Sanusi
Asali: Facebook

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, ya jagoranci Sallar Jumaa a Awe (Hotuna)
Tsohon Sarkin Kano, Sanusi
Asali: Facebook

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi, ya jagoranci Sallar Jumaa a Awe (Hotuna)
Tsohon Sarkin Kano, Sanusi
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng