Mayakan Boko Haram sun sha ruwan bama-bamai ta sama a dajin Sambisa

Mayakan Boko Haram sun sha ruwan bama-bamai ta sama a dajin Sambisa

Rundunar Sojan saman Najeriya ta bankado wani sabon mafakar yayan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a wani kauye dake Bula Korege inda suke sake tattaruwa a cikin dajin Sambisa, sai dai rundunar ta sake tarwatsa su.

Jaridar Punch ta ruwaito daraktan watsa labaru na rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, inda yace yan ta’addan na kokarin kai ma Sojoji da fararen hula hari ne a lokacin da rundunar Sojan saman ta bankado su.

KU KARANTA: Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Hakan yasa rundunar tura jiragenta na yaki domin tarwatsa yan ta’addan, inda suka yi musu ruwan bama-bamai inda suka kashe mayakan Boko Haram da dama tare da lalata mafakar tase tare da makamansu da sauran kayan aiki.

“A cigaba da aikin Operation Decisive Edge, rundunar Sojin sama na Operation Lafiya Dole ta halaka mayakan Boko Haram da dama a kauyen Bula Korege dage gefen dajin Sambisa a jahar Borno.

“An kai harin ne a sawu biyu bayan samun labarin yan ta’addan sun koma wani sabon mafaka a kauyen, kuma suna shirin kaddamar da hare hare a kan sansanonin Sojojin kasa da jama’an gari, don haka rundunar ta tura jiragenta na yaki don kalubalantar yan ta’addan.

“Koda jiragenmu suka sansanin, sun tabbatar da hada hadar yan ta’adda a cikinta, daga nan suka shiga cilla musu bama-bamai tare da ruwan wuta inda suka kashe yan ta’adda da dama tare da lalata mafakar,.

"Bayan sawun farko, an hangi yan ta’addan sun sake tattaruwa a wani sashin sansanin, amma duk da haka sai da jiragen suka sake binciko su, sa’annan suka mitsitstsikesu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel