Yanzu-yanzu: Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi - Ministan Lafiya

Yanzu-yanzu: Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi - Ministan Lafiya

Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Enahire, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a sallami dan kasar Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya.

TVC News ta ruwaito cewa Ministan lafiyan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja yayinda yake tattaunawa da jami'ai daga kasashen waje kan matakan da gwamnatin tarayya ke dauka wajen dakile yaduwar cutar.

Ministan ya jaddada cewa har yanzu mutane biyu kadai ke dauke da cutar a Najeriya.

Yanzu-yanzu: Dan Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya ya samu sauki, za'a sallameshi - Ministan Lafiya
Ministan Lafiya
Asali: UGC

A baya mun kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Coronavirus Najeriya ya murmure kuma za'a sallameshi daga inda aka killaceshi nan ba da dadewa ba.

Sakataren yada labaran gwamnan, Kunle Somorin, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kamfanin Simintin, Lafarge PLC, karkashin jagorancin shugabanta, Khaleed El Dokani, a ofishinsa dake Oke-Mosan, Abekuta.

Yace: "Mara lafiyan yana cikin halin lafiya kuma za'a sallameshi nan ba da dadewa ba."

Gwamnan ya bayyana cewa cutar babbar kalubale ce ga jihar Ogun, a matsayinta na jihar manyan masana'antun Najeriya.

Ya lashi takobin cewa gwamnatinsa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen takaita yaduwar cutar ba.

Mutan duniya gaba daya a halin yanzu na gujewa wuraren da akwai taron jama'a, da dama sun soke tafiye-tafiye, yayinda wasu suka koma zaman gida gaba baya gudun kamuwa da cutar Coronavirus da ta addabi duniya.

Kawo yanzu, akalla mutane 114,000 sun kamu da cutar kuma 6000 sun rigamu gidan gaskiya kuma ta ratsa akalla kasashe 90 a fadin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel