Yanzu-yanzu: Buhari ya umurci El-Rufai ya baiwa Sanusi Lamido mukami

Yanzu-yanzu: Buhari ya umurci El-Rufai ya baiwa Sanusi Lamido mukami

Hadimin shugaba Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa shugaban kasa ne ya umurci gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya baiwa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, mukami.

Hadimin ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita inda ya yi mamakin har yanzu babu wanda ya yabawa Buhari kan mukaman ban girman da aka baiwa Sanusi ba tun lokacin da ya sauka daga mulki.

Bashir yace "Har yanzu ban ga kowa yana yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan mukaman da aka baiwa Sanusi kwanan nan ba, shi ya umurci dan gaban goshinsa, Mallam Nasir El-Rufai ya bashi.”

Yanzu-yanzu: Buhari ya umurci El-Rufai ya baiwa Sanusi Lamido mukami
Yanzu-yanzu: Buhari ya umurci El-Rufai ya baiwa Sanusi Lamido mukami
Asali: UGC

Mun kawo muku cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta alanta tunbukekken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Cansalan jami'ar jihar Kaduna KASU.

Sanusi, zai maye gurbin Cansalan jami'ar na farko, Hakimin Moroa, Tagwai Sambo, wanda yake rike da mukamin tun shekarar 2005.

Sanarwa daga gidan gwamnatin jihar yace

“A madadin gwamnati da alummar jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, na farin cikin na Muhammadu Sanusi II a matsayin Cansalan jamiar jihar Kaduna.“

Hakazalika, Gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammadu Sanusi II gurbin aiki KADIPA, cibiyar habaka kasuwancin jihar.

A wata takarda da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.

An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna. Bankin Duniya kuwa ya kalla cibiyar a matsayin ta farko a fannin kasuwanci a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel