Faduwar farashin mai: A shiryawa shiga wani irin hali mai wuya - Mele Kyari, shugaban NNPC

Faduwar farashin mai: A shiryawa shiga wani irin hali mai wuya - Mele Kyari, shugaban NNPC

Dirakta Manajan kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, a ranar Laraba ya bayyana cewa akwai barazana ga tattalin arzikin Najerya muddin ba a shawo kan matsalar faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya da cutar Coronavirus ba.

Yayinda yake jawabi a taron shawo kan lamarin da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya shirya, Kyari ya ce cutar Coronavirus da faduwar farashin manyan kalubale ne ga tattalin arzikin kasa.

An shirya zaman ne bayan farashin man fetur a kasuwar duniya ya sauko daga $57 zuwa $30 ga gangan.

A jawabin, ya ce a yanzu haka, akwai jirgaen ruwa 12 dauke da iskar gas na sayarwa amma babu masu saya saboda faduwar farashin da kuma cutar Coronavirus.

Ya ce na danyen man fetur ya fi muni saboda ”a yau, akwai jiragen ruwa 50 dauke da danyen mai amma basu samu sauka ba.”

”Hakan na nufin cewa yan kasuwan mai basu san inda zau kai danyen man ba. A jiya, kasar Iraqi ta rage farashin man ta da $5 yayinda kasar Saudiyya ta rage na ta da $8.”

”Saboda haka idan kana sayar danyen man ka a farashin $30 sannan ka rage da $8, ka ga $22 ya rage kenan.”

”Wannan babban matsalan zai iya sauki ga kasashe masu tace man fetur irinsu Saudiyya,.. amma ba zai taba yiwuwa ba a Najeriya.”

”Saboda haka ku shiryawa matsala na tsawon watanni 3, ko da farashin ya koma $58, akwai bashin da sai an biya na mai.”

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar Juma'a, 6 da Maris, maimakon yarjejeniyar da aka bukaci yi, an yi baran-baran a ganawar saboda kasar Rasha ta ki amincewa da rage adadin man feturin da zata rika fitarwa kuma hakan bai yiwa Saudiyya dadi ba.

Ba tare da bata lokaci ba kasar Saudiyya ta karya farashin man feturin da kimanin kashi 30%.

A ranar Juma'a da aka kammala ganawar, farashin gangar man fetur a kasuwar duniya ta fado daga $50 zuwa $45, amma a ranar Litinin, ta fado warwas zuwa $31.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel