Yanzu-yanzu: Bayan sauke shi daga mulki, gwamnatin Kaduna ta bawa Sanusi II babban mukami

Yanzu-yanzu: Bayan sauke shi daga mulki, gwamnatin Kaduna ta bawa Sanusi II babban mukami

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba Muhammadu Sanusi II gurbin aiki bayan tube masa rawani da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin. Ta bashi gurbi ne a KADIPA, cibiyar habaka kasuwancin jihar.

A wata takarda da ta fito daga gidan Kashim Ibrahim, Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da kafa shugabannin cibiyar KADIPA din.

An kafa cibiyar ne a 2015 kuma tana kan gaba ne wajen habaka kasuwancin jihar tare da saukakawa kasuwanci a jihar Kaduna. Bankin Duniya kuwa ya kalla cibiyar a matsayin ta farko a fannin kasuwanci a Najeriya.

Sanarwar da mai bawa gwamna shawara a fanin watsa labarai, Muyiwa Adekeye ya aike wa Premium Times a ranar Talata ta ce, “Malam Nasir El-Rufai ya amince da zaben mai martaba, Muhammadu Sanusi II zuwa shugabancin KADIPA. Cibiyar ta samu shugabancin mataimakiyar gwamnan tare da sauran jiga-jigai a gwamnatin jihar."

Yanzu-yanzu: Bayan sauke shi daga mulki, gwamnatin Kaduna ta bawa Sanusi II babban mukami
Yanzu-yanzu: Bayan sauke shi daga mulki, gwamnatin Kaduna ta bawa Sanusi II babban mukami
Asali: UGC

“Gwamna Nasir El-Rufai na fatan cin gajiyar gogewa da kwarewar Sanusi wanda ya gina ginshiki a fannin tattalin arziki a duniya kafin zamansa sarki. Malam Nasir El-Rufai ya ce jihar Kaduna na tsananin farin ciki da alfaharin samun aikin mutum kamarsa," in ji shi.

DUBA WANNAN: Buri na na karshe a rayuwa shine in mutu a kan kujerar sarautar Kano - Sanusi II

Ya cigaba da cewa, “Ya kara da jaddada cewa babu shakka sabbin shugabannin KADIPA din zasu kara habaka cibiyar ta yadda zata jawo hankalin masu zuba hannayen jari. Ya kara da cewa mambobin da aka zabo an tsamosu ne tare da kiyayewa."

Ga jerin sunayen shugabannin KADIPA din kamar haka:

1. Mataimakiyar gwamna, Dr. Hadiza Balarabe Chairman

2. Mai martaba, Muhammadu Sanusi II Vice-Chairman

3. Balarabe Abbas Lawal, Sakataren gwamnatin jihar

4. Bariatu Y. Mohammed, Shugaban ma’aikata

5. Jimi Lawal, Babban mai bada shawara

6. Aisha Dikko, Kwamishinan shari’ar jihar Kaduna

7. Idris Nyam, Kwamishinan kasuwanci, kirkirre-kirkire da fasaha

8. Fausat Ibikunle, Kwamishinan gidaje

9. Thomas Gyang, Kwamsihinan tsari da tattali

10. Farida Dankaka, KACCIMA

11. Amal Hassan, Bangaren ma’aikatu maus zaman kansu

12. Hafiz Bayero, shugaban hukumar habaka kasuwannin jihar Kaduna

13. Altine Jibrin, Babban daraktan KADGIS

14. Umma Aboki, Sakataren, KADIPA

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel