Yanzu-yanzu: Babu wani taron kwamitin zartarwar APC da za'ayi ranar 17 ga Maris - Kakakin jam'iyyar

Yanzu-yanzu: Babu wani taron kwamitin zartarwar APC da za'ayi ranar 17 ga Maris - Kakakin jam'iyyar

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Asabar ta yi watsi da rahoton cewa an kira ganawar majalisar zartarwar jam'iyyar na gaggawa domin tsige shugabanta, Adams Oshiomole.

Hakan ya bayyana ne a jawabin Kakakin jam'iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu da mai bada shawara kan harkokin doka, Babatunde Ogala, suka rattafa hannu.

A bangare guda, Akwai yiwuwar nesa ta zo kusa ga Kwamared Adams Oshiomhole a matayinsa na shugaban jam'iyyar APC na kasa bayan da gwamnonin jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) suka bukaci Kwamitin zartarwa na kasa na jam'iyyar ta maye gurbin sa nan take biyo bayan dakatar da shi da kotu ta yi.

Gwamnonin ta bakin Direkta Janar na Kungiyar Gwamnonin na APC, Salihu Lukman a ranar Juma'a 6 ga watan Maris sun bukaci Oshiomhole ya yi murabus daga mukaminsa.

Magoya bayan gwamna Godwin Obaseki daga jam'iyyar ta APC reshen jihar Edo sun shiga sun fita har sai da aka dakatar da Oshiomhole daga mazabarsa ta karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar.

Wata babban kotun tarayya a Abuja a ranar Laraba ta jadadda hukuncin da jiga-jigan jam'iyyar na APC reshen jihar Edo suka yi na dakatar da Oshiomhole.

Shugabanin na APC sun ki amincew da yunkurin da Oshiomhole ya yi na neman wata kotun tarayya a jihar Kano ta sake dakatarwar da aka yi masa.

Gwamnonin sun ce kafin lokacin da za a warware rikicin jam'iyyar, sun ce ya kamata ayi amfani da sashi na 17 na kundin tsarin jam'iyyar da ya ce ba zai yi wu a bar wata kujera babu wanda zai yi rikon kwarya ba idan an dakatar da mai ita.

Kafin yanzu, akwai jita-jitar cewa Sanata Abiola Ajimobi zai maye gurbing Oshiomhole kafin a warware rikicin jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel