An kaddamar da feshi da tsaftace Masallacin Harama na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona (Hotuna da bidiyo)

An kaddamar da feshi da tsaftace Masallacin Harama na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona (Hotuna da bidiyo)

Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin babban limami, Sheikh Abdur-Rahman As-Sudais ta kaddamar da feshi da tsaftace Mataaf na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona.

Mabiya addinin Islama a fadin duniya sun yi mamakin hakan inda da dama suka ce wannan shine karo na farko da zasu ga Masallacin Harami babu kowa.

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah da ziyarar Masallacin Annabi mai girma ga dukkan yan kasar da mazauna sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta dau matakin ne domin takaita yaduwar cutar a kasar mai alfarma.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta alanta cewa a mayarwa dukkan wadanda suka biya kudin Umrah kudadensu.

Kalli hotunan da bidiyon:

An kaddamar da feshi da tsaftace Masallacin Harama na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona (Hotuna da bidiyo)
Mataaf
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Kungiyar kiwon Lafiya ta duniya WHO ta shawarci jama’a da su rinka amfani da naurorin zamani wajen bukatunsu na kudi, domin kudi kan iya jawo yaduwar coronavirus.

Cutar Coronavirus zata iya zama akan kudi na tsawon kwanaki, Kungiyar kiwon lafiya tayi gargadi a daren Litinin.

Cutar Coronavirus zata iya yaduwa ta hanyar abubuwan da suke dauke da cutar da kuma haduwa da wadanda suke dauke da cutar, cewar kungiyar WHO.

"Domin hana yaduwar cutar, mutane su rinka amfani da naurorin zamani domin gudanar da bukatunsu na kudi bayan haka kuma su wanke hannayensu bayan sun taba kudin" cewar mai Magana da yawun kungiyar WHO.

Bankin Kasar Ingila ta gano cewa kudi kan iya daukar kananan kwayoyin cuta, kuma ta karfafa akan yawan wanke hannaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel