An sake killace wani dan Najeriya da ake zargin yana dauke da Coronavirus - Gwamnatin Legas

An sake killace wani dan Najeriya da ake zargin yana dauke da Coronavirus - Gwamnatin Legas

Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce an killace wani ɗan Najeriya da ya dawo daga kasar Faransa a Cibiyar Kula da Cututtuka masu Yaɗuwa da ke Yaba, Legas.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba, Abayomi ya ce wata an turo mutumin ne zuwa cibiyar daga wani asibitin kuɗi a Legas.

Kwamishinan ya ce zai sanar da sakamakon gwajin da aka yi wa mutumin da zarar an kammala.

Abayomi ya ce, "Ɗan Najeriya ne da ya tafi kasar Faransa, ya yi kwanaki bakwai a Faransa sannan ya dawo Legas kwanaki uku da suka gabata kuma yana fama da ciwon kai da matsalar numfashi.

Coronavirus: An sake killace wani dan Najeriya - Gwamnatin Legas
Coronavirus: An sake killace wani dan Najeriya - Gwamnatin Legas
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

"Hakan ya faru ne saboda ya ziyarci kasar da akwai yiwuwar yaduwar cuta tsakanin mutane, akwai yiwuwar mura ce kawai amma akwai yiwuwar cutar Coronavirus ce."

"An killace shi yanzu, ana yi masa gwaje-gwaje a halin yanzu, ina jiran sakamakon gwajin," in ji Abayomi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel