Magidanci ya kashe kansa bayan ya yiwa 'ya'yanshi gargadi a kan sharrin mata

Magidanci ya kashe kansa bayan ya yiwa 'ya'yanshi gargadi a kan sharrin mata

- Wani tsohon ma'aikacin five-star otal da ke Legas ya kashe kan shi. Lamarin ya faru ne a gidan shi da ke yankin Adamo da ke Ikorodu

- An zargi cewa Taiwo ya dauki rayuwar shi ne bayan wani sirrin bashi da ke tsakanin shi da wata mata don kasuwanci

- Da farko dai, mamacin ya fara tattara 'ya'yan shi sannan ya basu shawara a kan su yi taka-tsan-tsan da matar da zasu aura a rayuwarsu

Wani tsohon ma'aikacin five-star otal da ke Legas ya kashe kan shi. Lamarin ya faru ne a gidan shi da ke yankin Adamo da ke Ikorodu a jihar Legas. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa mamacin ya rufe kan shi ne a dakin baccin shi sannan ya sha maganin kwari mai suna Sniper bayan ya bar wasiyya a rubuce.

An zargi cewa Taiwo ya dauki rayuwar shi ne bayan wani sirrin bashi da ke tsakanin shi da wata mata don kasuwanci, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Da farko dai, mamacin ya fara tattara 'ya'yan shi sannan ya basu shawara a kan su yi taka-tsan-tsan da matar da zasu aura a rayuwarsu.

"Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a titin Akpofure da ke Adamo a Ikorodu. Ana zargin mutuwar na da nasaba ne da bashi da kuma matsalar iyali kamar yadda wasiyyar shi ta bayyana.

Magidanci ya kashe kansa bayan ya yiwa 'ya'yanshi gargadi akan sharrin mata

Magidanci ya kashe kansa bayan ya yiwa 'ya'yanshi gargadi akan sharrin mata
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Fasto ya bawa mabiyansa maganin bera don ya tabbatar da imaninsu sun sha sun mutu

"An zargi cewa ya sha guba ne don dakin shi yana ta warin Sniper din. Yayi magana da 'ya'yan shi kafin ya rufe kan shi a daki. A lokacin da matar shi ta tambaya yaran shi inda yake, sun sanar da ita yana dakin shi. Bayan kwankwasawar da babu martani, sai tayi amfani da makulli ta bude kofar inda ta tarar da gawar mijinta a gado," wata majiya ta ce.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Legas,, DSP Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike a kan hakan.

"An dauke gawar inda aka mika ta ma'adanar gawawwaki don a duba sanadiyyar mutuwar ta," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel