Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban

Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban

- Wani bidiyo mai ciike da bada dariya na dan sanda da matukin tasi ya bazu a soshiyal midiya

- A bidiyon, na dan sanda sama sagale a kan motar tasi din yayin da direban ke tukawa

- An gano cewa dan sandan yah aye saman motar ne yayin da dirban ke tukawa duk a kokarinsa na tsayar da motar

A Najeriya dai, mutane sun dade da cire rransu daga lamrin masu khaki. A saboda hakan ne ake yawan tozartawa tare da rashin ganin girman ‘yan sanda mata da maza balllantana a lokutan da ba wani abun asha suka yi ba.

Wasu ‘yan sandan maza da mata sun saba tatsar masu ababen hawa na haya a kowacce damar da suka samu duk kuwa da ana ci gaba da cewa dan sanda abokin kowa ne.

Direbobi da yawa kuwa sun dade da gundura da halyayya tatse su da ‘yan sandan ke da ita a duk damar da suka samu.

Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban

Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

A cikin kwanakin nan ne kuwa wani bidiyon ban dariya na dan sanda da direban tasi yake ta zagaya kafafen sada zumuntar zamani. A takaice dai, dan sandan ne aka gani dare-dare a saman motar yana rike da ita don gudun kuskuren da zai say a rasa rayuwarsa.

Lamarin ya faru ne a garin Abuja kuma an gano cewa dan sandan dakan shi ya haye saman motar don kokarin tsayar da direban tasin. Hakan kuwa bai yi aiki ba don direban ya ci gaba da tukinsa ba tare da nuna ya san abinda dan sandan yake yi ba.

Hakan ne kuwa ya tada wad an sandan hankali don a gaggauce ya kama gefe da gefen motar gudun kuskuren da zai yi ya rasa ransa.

A cikin kwanakin nan ne kuwa wani bidiyo ya bayyana wanda wata matar aure ke zane karuwar mijinta a dakin otal a jihar Benin.

Matar da ta damke karuwar ne tare da yi mata mugun duka har da yaga maya kayanta saboda mu’amalarta da mijinta. Dukan ya yi yawan da har matar ta kai ga yaga wa karuwar kayan sanya wa yayin da jami’an tsaro ke kokarin shawo kan matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel