Coronavirus: An killace yan kasar Sin hudu a Abuja

Coronavirus: An killace yan kasar Sin hudu a Abuja

Bisa ga matakan da ake dauka wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya, an killace ya kasar Sin hudu da suka shigo Najeriya a asibitin koyarwan jami'ar Abuja, birnin tarayya.

An killace yan kasar Sin din ne bayan an samesu da alamomin cutar huhu yayinda suka dira Najeriya a ranar Talata a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Wani jami'in sashe yada labaran asibiti, Mista Sule, ya bayyana cewa an kawosu asibitin ne misalin karfe 4:30 na yammacin Talata.

Ya ce an gwada su kuma ba'a samesu da cutar Coronavirus ba amma ba za'a sake su ba.

Yace: "Ba'a samu cutar a jikinsu ba bayan gwaji amma za'a killacesu na tsawon kwanaki 14 domin tabbatarwa"

Yayinda aka tuntubi shugaban asibiti, ya ki tsokaci kan lamarin.

Coronavirus: An killace yan kasar Sin hudu a Abuja
Coronavirus: An killace yan kasar Sin hudu a Abuja
Asali: Twitter

A bangare guda, Wata Likitar kananan kwayoyin cututtuka, Adeola Fowotade, yace sauyin yanayi na zafi a Nigeria kan iya taimakawa wajen dakile da yaduwar cutar Coronavirus.

Fowotade, mai aiki a babban asibitin UCH dake birnin Ibadan, ta bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN ne a Ibadan.

Bisa ga bayaninta, wasu daga cikin gwanaye suna tunanin Coronavirus zata iya dabi’antuwa da cutar mura, wacce take aukuwa duk shekara a yanayin sanyi, idan haka ya tabbata, zafin Nigeria kan iya hana yaduwar coronavirus.

Tace: “Muna kyautata zaton cewa idan Covid-19 cutar layin numfashi ne, to zai iya bin sahun hakan. Akwai yiwuwan idan yanayi ya sauya a kasashen da ke fama da sanyo yanzu, abubuwan zau yi sauki.”

“Amma mu masu yanayi mai zafi, muna imanin cewa nan ba da dadewa ba cutar zai gushe.”

“Dalili shine kwayar cutar diga takeyi kuma saboda haka ba zata iya tafiya mai nisa ba. Kasancewarta haka, ba zatayi rayuwa cikin zafi ba.”

Amma ta yi kira ga kowa musamman ma’aikatan kiwon lafiya su cigaba da mayar da hankali wajen tsafta da lura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel