Yanzu-yanzu: Kuma dai, an dage zaman sake duba shari'ar gwamnan Zamfara a kotun koli

Yanzu-yanzu: Kuma dai, an dage zaman sake duba shari'ar gwamnan Zamfara a kotun koli

Kotun koli, a ranar Litinin, ta sake dage zaman sauraron bukatar jam'iyyar All Progressives Congress APC inda ta bukaci kotun koli ta sake duba shari'ar da ta yanke ranar 24 ga Mayun, 2019 inda ta kwace dukkan kujerun da yan takaran suka lashe a jihar Zamfara.

Kotun ta ce a dawo ranar 17 ga Maris domin cigaban da zaman.

Jamiyyar APC a jihar ta shigar da kara ne ta lauyanta, Robert Clarke, inda ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin da ta sake ranar 24 ga Mayu, 2019 na sallamar dukkan wadanda suka lashe zabe karkashin APC saboda basu gudanar da zaben fidda gwani ba.

Za ku tuna cewa ana saura kwanaki biyar rantsar da sabon gwamnan jihar Zamfara, kwamitin Alkalan kotun koli biyar karkashin CJN Tanko Muhammad sun yi ittifakin cewa jamiyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga dokokin jamiyyar saboda haka dukkan kuriun da APC ta samu a zaben ya zama banza.

Sakamakon haka, wanda ya zo na biyu a zaben, Bello Matawalle na PDP ya zama zakaran zabe kuma a ranstar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.

Yanzu-yanzu: Kuma dai, an dage zaman sake duba shari'ar gwamnan Zamfara a kotun koli
kotun koli
Asali: UGC

A bangare guda, Kotun koli, a ranar Litinin, ta sake dage zaman sauraron bukatar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da dan takararta Emeka Ihedioha na sake duba shari'ar zaben gwamnan jihar Imo.

Kotun ta ce a dawo gobe (Talata) domin cigaban da zaman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel