Hotunan mutumin kasar Italiya da ya kawo Coronavirus Najeriya

Hotunan mutumin kasar Italiya da ya kawo Coronavirus Najeriya

Wasu disassun hotunan dan kasar Italiya da aka kebe a asibitin jihar Legas a kan cutar Coronavirus sun bayyana. Kwamishinan lafiyar jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ne ya wallafa hotunan a shafinsa.

Farfesa Abayomi ya ziyarci mutumin da aka kebe din inda ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na tuwita.

Kamar yadda ya walllafa, “Na ziyarci mara lafiyar da ke dauke da cutar COVID-19 a asibiti inda jami’an kiwon lafiya ke kula da shi. Na yi magana da shi tare da tabbatar masa da cewa gwamnatin jihar Legas ta shirya tsaf don shawo kan matsalarsa.”

“A yayin da na ziyarci asibitin, na yi amfani da damar wajen zagaya asibitin da kuma ganin gyaran da aka yi a dakunan. A nan da kwanaki kadan za a kammala gyaran. Na gamsu da gyaran tare da kokarin asibitin,” ya kara da cewa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Masu binciken kimiyya a kasar Isra'ila sun gano riga-kafin Coronavirus

Amma kuma a yau, jaridar The Punch ta ruwaito yadda wanda aka killace din a asibitin jihar Legas din ya yi yunkurin guduwa sakamakon sauro da zafin da suka addabesa a inda aka killace shi.

Mara lafiyan ya nuna damuwar shi a kan yadda wajen da aka kebance shi yake, wata majiya ta ce.

Wani babban ma'aikacin lafiya da ya yi magana da wakilin jaridar The Punch a ranar Juma'a, ya jajanta yadda wajen yake. Ya ce "hukumomi ba su cika alkawarin da suka dauka ba."

Mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat a ranar Juma'a ya ce gwamnatin jihar ta gina wajen kula da marasa lafiyan kuma wanda aka gano yana dauke da cutar na samun sauki.

Hamzat ya ce, "a dakin da yake, akwai gadaje 100 kuma a halin yanzu gado daya ne aka hau. Muna fatan ba za ta ci gaba da yaduwa ba. A shirye muke kuma muna da kayan aiki. Mara lafiyan yana samun sauki don likitoci sun ce yana samun lafiya."

Amma kuma sai ma'aikacin lafiyan ya sanar da cewa mara lafiyan na korafin zafi da sauro. Hakazalika, ba a tanadarwa ma'aikatan lafiyan kayan kariya ba. Ya ce, "mara lafiyan ya so tserewa jiya Alhamis. Dan kasar Italia din wanda injiniya ne ya fusata da halin da yake ciki. Sauro da zafi duk sun ishe shi. Babu komai a dakin banda gado da wajen ajiye-ajiye. Ya kusan guduwa kuma har yanzu yana barazanar hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel