Sojoji sun kama 'yar bindiga 'na rawa da AK-47 rataye a wuyar ta' a Kaduna

Sojoji sun kama 'yar bindiga 'na rawa da AK-47 rataye a wuyar ta' a Kaduna

Dakarun sojojin Najeriya sun kama wata da ake zargin 'yan bindiga ce, Zainab Abubakar, a Unguwan Salaha, Mararaban Jos a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Rundunar sojin ta ce a ranar Alhamis cewa binciken da aka fara gudanarwa a wayar salular wace ake zargi 'ya nuna ta tana tika rawa rataye da bindiga AK - 47 a wuyan ta.'

The Punch ta ruwaito cewa Dakarun sojojin 1 Division Garrison a karkashin Operation Mesa ta kama Zainab Abubakar ne a ranar Litini.

Mai kula da sashin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Kwanel Aminu Iliyasu, ya tabbatar wa manema labarai kama wacce ake zargin inda ya ce, "Dakarun 1 Division Garrison ta kama wata 'yar bindiga mace a Unguwan Salaha a Mararaban Jos. Binciken da aka gudananar da fari ya nuna bidiyo a cikin wayar ta tana tika rawa da bindiga AK-47 a wuyan ta wurin wani taro.

Sojoji sun kama 'yar bindiga mace tana rawa da AK-47 rataye a wuyar ta
Sojoji sun kama 'yar bindiga mace tana rawa da AK-47 rataye a wuyar ta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata mata ta mutu bayan kammala zina da saurayinta dan sanda

"Dakarun sojojin ta suka kai sintiri a kusa da kauyen Kirsa a karamar hukumar Anka a jihar Zamfara sun tare wani mai babur da ke dauke da wata budurwa.

"Sai dai mai tuka babur din ya saki babur din sannan budurwar ta tsere ta shiga daji.

"Bayan hakan sojojin sun kama budurwar, sun kwato AK-47 guda daya daga hannun ta, wani AK-47 din da harsashi guda 30 masu tsawon 7.65mm da kuma babur kirar Honda.

"Kazalika, a ranar 25 ga watan Fabrairun 2020, dakarun sojojin 1 Division bayan samun sahihan bayannan sirri sun kama wasu 'yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu mutane a Niger a kwanakin baya.

"Dakarun sojojin sun gano inda 'yan bindigan suke a Chikwale a karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna. Miyagun sun yi watsi da wadanda suke garkuwa da su sun tsere cikin daji.

"Sojojin sun ceto wani Abubakar da 'yan bindigan suka yi garkuwa da shi, sun kuma kwato AK-47 guda biyu, wayoyin salula 36, na'uarar lantarki mai aiki da rana, jakunkuna dauke da tufafi da kayan abinci da rigar sanyin ta sojoji."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel