Hattara dai Coronavirus: Na biyo ta filin jirgin sama kuma ba'a tantance mutane masu shiga Najeriya - Sanata Boro

Hattara dai Coronavirus: Na biyo ta filin jirgin sama kuma ba'a tantance mutane masu shiga Najeriya - Sanata Boro

Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ajayi Boroffice ta bayyana cewa babu abinda akeyi domin kare Najeriya da annobar cutar Coronavirus.

Yayinda yake magana a zauren majalisar yau Alhamis, Sanata Boroffice yace yayinda ya dira babban filin jirgin saman kasa da kasa na Abuja daga kasar Afrika ta kudu ranar Laraba, bai ga ana duba masu shiga kasar ba.

Ya ce innama yar takarda ake baiwa mutane su rubuta ko suna da lafiya ko basu da lafiya.

Ya kara da cewa a kasar Afrika ta kudu da yaje, sai da aka tantancesu kafin sauka daga cikin jirgin.

Hattara dai Coronavirus: Na biyo ta filin jirgin sama kuma ba'a tantance mutane masu shiga Najeriya - Sanata Boro
Hattara dai Coronavirus
Asali: Twitter

Yace: "Ina kasar Afrika ta kudu ranar Juma'a, kuma na dawo jiya. Saboda lamarin Coronavirus din nan, dukkan kasashen duniya na daukan matakan kiyaye shigan cutar kasashensu."

"A Afrika ta kudu, ba'a bari muka sauka daga cikin jirgi ba na tsawon mituna 30,"

"Jami'an kiwon lafiya sun shigo cikin jirgin kuma suka tantance kowa kafin aka amince muka shiga cikin kasar amma yayinda na dawo jiya a filin jirgin Nnamdi Azikwe, babu wanda ya tantancemu."

"Kawai wata yar takarda aka bamu mu rubuta ko munada lafiya ko bamu da shi. Ta yaya zaku san ban da lafiya. Abin da ban toro."

Sanatan ya ce gaskiya ya kamata a yi tsayin daka wajen hana cutar shigowa Najeriya.

Mun kawo muku rahoton cewa Mataimakiyar shugabar kasar Iran kan harkakokin mata da Iyali, Masoumeh Ebtekar, ta kamu da cutar Coronavirus da ta addabi duniya, jaridar kasar ta ruwaito.

Masoumeh Ebtekar ce mambar majalisar zartarwar kasa ta farko da zai kamu da cutar tun lokacin da ta bulla a Iran.

A yau, shugaban kwamitin harkokin wajen Iran na majalisar dokokin kasar, Mojitaba Zolnour, ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa shi ma ya kamu da cutar ta Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel